Taraba: An shawo kan rikicin garin Wukari
November 8, 2015Talla
Rahotanni daga Wukari na jihar Taraba na cewa wata tarzoma ta barke a garin tun a daren jiya jim kadan bayan da wani hukunci kotu ya ce Senata Aisha Alhasan ce ta lashe zaben gwamna a jihar. Wakilin DW a Yola Muntaqa Ahiwa wanda ya isa a cikin jihar ta Taraba, ya ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen garin sun tabbatar masa da cewa, da tsakar daren jiya an ji harbe-harben bindigogi.
Wannan rikici dai ya yi sanadiyyar rayukan mutane, da kawo yanzu babu cikakken adadi, daura da asarar dukiyoyi sakamakon ko-konen da aka ayi.
Sai dai ya ce ya zuwa safiyar wannan Lahadi kura ta lafa bayan da aka kai jami'an tsaro a garin.