1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mittelmeerunion EU

Hagedorn, Anke (DW Brüssel) NEUJuly 12, 2008

Wannan dai wani gagarumin shiri ne na shugaban Faransa Nikolas Sarkozy

Shugaba Nikolas SarkozyHoto: AP


A ranar lahadi ake gudanar da taron ƙolin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai da takwarorinsu na yankin Tekun Bahar Rum a birnin Paris. Taron zai bawa Turai ƙarin angizo a yankin Gabas Ta Tsakiya tare da inganta tuntuɓar juna tsakaninta da ƙasashen Larabawa na wannan yanki. To sai dai Larabawa na nuna shakku ga wannan shiri wanda shugaban Faransa Nikolas Sarkozy ya gabatar.


Shrin kafa Tarayyar ƙasashen Tekun Bahar Rum ya kasance wani gagarumin aiki na shugaban Faransa Nikols Sarkozy, inda tun a lokacin yaƙin neman zaɓen shugabancin Faransa ya mayar da hankali ga wani shirin kafa wata tarayya tsakanin Turai da Afirka. Yanzu a matsayinsa na shugaban EU Sarkozy na son ya aiwatar da wannan shiri. Jim kaɗan gabanin wannan taro karon farko na tayyarar ƙasashen Tekun Bahar Rum a birnin Paris Sarkozy ya sake jadada muhimmancin wannan aiki.


Sarkozy ya ce "Muna aiki dare da rana akan wannan tarayya ta ƙasashen Bahar Rum. Wannan wani abu ne da na ƙuduri aniyar sa kuma da ina maraba da dukkan shugabannin da ke halartar wannan taro a Paris. Wannan wani albishir ne ga shirin samar da zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya."


Ko da yake ba dukkan shugabannin ƙasashen Larabawa ne ke halartar taron ba, amma an jiyo shugaban majalisar dokokin Turai Hans-Gert Pöttering yana maraba da wannan dama da aka samu da zata ƙarfafa haɗin kai tsakani.


Pöttering ya ce "Majalisar Turai za ta tsaya ta ga an samu kyakkyawan sakamako a wannan taro musamman a batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, kare muhalli, sufuri da kuma al´adu. Taron dai shi ne zaure guda ɗaya da zai haɗa Isra´ila da Falasɗinawa shi ya sa majalisar Turai ta na ba da cikakken goyon bayanta."


Shi ma a nasa ɓangaren shugaban hukumar zartaswan EU Jose Manuel Barroso ya ƙarfafa guiwar Sarkozy ne yana mai cewa.


Barroso "Ina mai jaddada muhimman matakai biyu na shugabancin Faransa ga ƙungiyar EU. Wato manufar tsaro ta bai ɗaya tsakanin ƙasashen EU da kuma tarayyar ƙasashen Bahar Rum. Wannan zai bawa EU damar taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasar duniya."


To sai dai shirin kafa wannan tarayya kamar yadda za a tattauna a birnin Paris ya banbanta da ra´ayin Sarkozy na kafa tarayyar da farko. Alal misali Jamus ta dage sai da aka yi watsi da aniyar Faransa ta mayar da tarayyar karƙashin jagorancinta ita kaɗai. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta matsa ƙaimi aka maido da wannan tarayyar ƙarkashin tsare-tsare ƙungiyar EU.