1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tarayyar Afirka ta ce an tafka magudi a zaben Tanzaniya

November 6, 2025

Kungiyar Tarayyar Afirka, ta zargi hukumomin kasar Tanzaniya da tafka magudi a babban zaben kasar da ya bai wa Shugaba Samia Suluhu Hassan nasara. Masu sa ido na kungiyar ne suka bayyana haka.

Habasha: Taron shugabanni da manyan jami’an gwamnati na Kungiyar Tarayyar Afirka.
Habasha: Taron shugabanni da manyan jami’an gwamnati na Kungiyar Tarayyar Afirka.Hoto: Solomon Muchie/DW

Masu sa ido a harkokin zabe na kungiyar Tarayyar Afirka sun ce sahihancin babban zaben Tanzaniya da aka gudanar a ranar 29 ga watan jiya ya samu cikas, inda suka gano wasu lokuta da aka cika akwatin zabe da kuri'un bogi.

Rahoton farko na kungiyar ya bayyana cewa an samu masu kada kuri'a da aka ba su takardun zabe fiye da daya, wasu kuma suka kada kuri'a ba tare da tabbatar da sunayensu a rajista ba.

Kungiyar ta ce an hana masu sa ido shiga wajen kirga kuri'u, abin da ya rage gaskiya da bude-bude a tsarin zaben.

Haka ma wasu wuraren zabe sun takaita wa masu sa ido lokacin aikinsu zuwa mintuna biyar kacal.

Rahoton ya kuma ambaci tashin hankali da harbe-harbe da rufe hanyoyi da kone-konen tayoyi a garuruwa da dama ciki har da Dar es Salaam babban birnin kasar.