1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Afirka ta ce babu kisan kiyashi a Najeriya

November 13, 2025

Kungiyar Tarayyar Afirka, ta karyata zargin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista a Najeriya. Shugaban kungiyar ne ya sanar da haka a birnin New York na Amurka.

Tambarin Tarayyar Afirka
Tambarin Tarayyar AfirkaHoto: Solomon Muchie/DW

Shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar Tarayyar Afirka AU, Mahmoud Ali Youssouf, ya karyata zargin da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan cewa ana aikata kisan kare dangi ga Kiristoci a arewacin Najeriya.

Da yake magana da ‘yan jarida a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Mahmoud Ali Youssouf ya ce babu wata hujja ko shaida da ke nuna cewa an taba samun irin wannan kisan kare dangi a yankin.

Ya jaddada cewa ya kamata mutum ya yi tunani sosai kafin ya fitar da irin wadannan kalamai, yana mai cewa mafi yawan wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hare-haren Boko Haram Musulmai ne  ba Kiristoci ba.

A farkon wannan watan, Donald Trump ya ba da umarni ga ma'aikatar tsaron Amurka da ta shirya yiwuwar daukar matakan soja idan har Najeriya ta gaza kawo karshen abin da ya kira kisan Kiristoci.