1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tshisekedi zai jagoranci kungiyar AU

February 2, 2021

Shugabannin kasashen Afirka sun zabi shugaban kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya gaji takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban AU.

Demokratischen Republik Kongo | Präsidenten Félix Tshisekedi in Kinshasa
Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango kana sabon shugaban Tarayyar Afirka na karba-karba, Félix Tshisekedi Hoto: Giscard Kusema

Yayin taron shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirkan AU na shekara-shekara ne dai, aka zabi Felix Tshisekedi a matsayin shugaban karba-karba na kungiyar ta AU. Sai dai shugaban na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, na shirin fara aikin ne a daidai lokacin da kasarsa take fama da tashe-tashen hankula. Hakan ya sanya ake ganin tilas sai Tshisekedi ya dage, ko da zai iya tunkarar rigingimu da nahiyar Afirka ke fama da su na siyasa da na ta'addanci, sakamakon yadda shi kansa kasarsa ke cikin wani yanayi na rikita-riktar siyasa baya ga masu tayar da kayar baya da suke dauke da makamai a gabashin kasar.

Karin Bayani: Shugaba Tshisekedi ya raba gari da Kabila

A makon jiya firaministan kasar Sylvestre Ilunga Ilukamba ya yi marabus, kafin nan kuma an tsige shugabar majalisar dokokin kasar Jeannine Mabunda daga mukaminta. Kawancen da ke tafiyar da mulki a kasar ta Kwango na FCC da CASH ya rushe, bayan da shugaban ya raba gari da jam'iyyun siyasar ciki har da ta tsohon shugaban Joseph Kabila. Yayin da a gabashin kasar ake ci gaba da gwabza yaki.
Shida daga cikin kasashe 10 da ake yake-yake a duniya dai na Afirka ne, misali Somaliya da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Libiya. Haka kuma rikicin 'yan ta'adda, ya dabaibaye kasashen yankin tafkin Chadi. Akwai kuma wasu bala'o'i da ake fama da su kama daga ambaliyar ruwa da kuma annobar corona. A bara kadai  a cikin watannin shida na farkon shekarar, mutane dubu 732 ne suka yi kaura daga gidajensu daga ciki dubu 718 saboda yake-yake dubu 14 sakamakon bala'o'i. Manazarta dai na ganin Tshisekedin na da kalubale a gabansa.

Kasashen Afirka da dama na fama da hare-haren ta'addanci,baya ga rikicin siyasaHoto: Reuters/F. Omar

Karin Bayani: Kamun ludayin shugaba Felix Tshisekedi

Duk da cewar shugabannin kasashen Afirka sun bayar da shugabancin na karba-karba na AU ga Felix Tshisekedi rashin cikka alkawarin da ya dauka ga 'yan siyar kasarsa, ka iya sanya shakkun ganin ya kai ga warware wasu rigingimu da Afirka ke fuskanta. Shi ne dai shugaban kasa na biyu a Kwango da ya samu matsayin na AU bayan Mubutu Sese Seko a shekara ta 1967.