Salon rayuwaTurai
Ko matakin EU na bai wa yara kariya zai yi wu?
July 14, 2025
Talla
Hukumar Tarayyar Turan ce ta sanar da hakan, inda ta ce za ta yi gwaji na wannan manhaja da za ta rinka tabbatar da ainihin shekarun yara. Zai a fara amfani da manhajar, a kasashen Denmark da Faransa da Spaniya da Girka da kuma Italiya. Tsarin dai zai hada sabuwar fasahar da katin shaidar zama dan kasa, na kasashen Tarayyar Turai na zamani da ake amfani da shi ta hanyar Internet na yaran. Tarayyar Turan ta ce za a fara amfani da tsarin a karshen shekara ta 2026 da ke tafe, wanda zai rinka tabbatar da ainihin shekarun yaro a kafar ta Internet.