1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta sake kakabwa Rasha takunkumi

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 16, 2022

Baya ga amincewa da kakabawa Rasha sabon takunkumi da shugabannin kasashen kungiyar EU suka yi, sun kuma amince da ci gaba da bai wa Ukraine tallafin kudi da yawansu ya kai Euro biliyan 18.

Beljiyam | EU | Taro | Rasha | Makamashi | Ukraine | Tallafi | Jamus | Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Nicolas Landemard/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Nan gaba a Ranar Litinin din makon gobe ministocin makamashin kasashen kungiyar ta EU za su yi wani taro na musamman, domin tattauna batun shawo kan matsalar farashin gas da Turan ke fuskanta. Sai dai kuma shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya nuna faragabar cewa rage farashin makamashin gas din, ka iya yin barazanar wajen samar da wadatacciyar iskar gas ga al'umma a wannan lokaci na tsananin sanyin hunturu da ake ciki.