1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

EU: Matakin toshe almundahana

Ramatu Garba Baba
June 1, 2021

Tarayyar Turai ta kaddamar da bikin bude ofishin babban mai gabatar da kara na Kungiyar tarayyar Turai da aka samar domin toshe dukkan wata almundahana da kudade a tsakanin kasashen kungiyar.

Rumänien Antie Regierungsproteste Pro EU Aktivist
Hoto: Getty Images/AFP/D. Mihailescu

Tarayyar Turai ta kaddamar da gudanar da bikin bude ofishin babban mai gabatar da kara na Kungiyar tarayyar Turai da aka samar domin toshe dukkan wata almundahana da kudade a tsakanin kasashen kungiyar. Ofishin da aka yi wa lakabi da suna EPPO da ke da hedkwata a birnin Luxemburg, ya tanadi kwararru da za su gudanar da aiyukan kula da asusun kungiyar tare da hana almundahana da kasafin kudin kungiyar. 

Shugabar ofishin, Laura Kovesi, ta ce, an kafa tarihi da wannan tsarin, na ganin su kare tattalin arzikin nahiyar Turan daga dukkan wata barazana, wanda ta ce, shi ne burin kowacce sahihiyar gwamnatin da aka kafa bisa tafarkin demokradiya. A wani bincike da kamfanin yada labaran Faransa ya gudanar, an gano cewa, asusun kungiyar na tafka asarar na kimanin euro miliyan dari biyar a duk shekara a sakamakon matsaloli, na cin hanci da rashawa ko almundahana da kuma kin biyan kudin haraji.