1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Tarayyar Turai ta yi tir da karuwar hare-hare a Darfur

November 13, 2023

Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da halin da ake ciki a yankin Darfur na Sudan, inda kashe kashe ya sake dawowa a baya-bayan nan abin da ke dagula lamura a yankin.

Wasu da ke ciki hali na tagayyara a Darfur
Wasu da ke ciki hali na tagayyara a DarfurHoto: ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi tir da karuwar tashe-tashen hankula da ake gani a yankin Darfur na kasar Sudan, tana mai gargadin cewa hakan ka iya kunna wata wutar kisan kiyashi.

Wata sanarwa ta ambato babban jami'in diflomasiyya na Tarayyar Turai Josep Borrell na cewa an kashe sama da mutum dubu guda 'yan asalin yankin Masalit cikin 'yan kwanakin nan a wasu sabbin hare-hare.

Yankin na Darfur dai ya fuskanci yaki a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2008, yakin kuma da ya yi sanadin salwantar rayukan mutane sama da dubu 300 wasu fiye da miliyan biyu kuwa suka rasa sukuni.

Rikicin da Sudan ta fada a ciki a watan Afrilun bana, sakamakon takaddama tsakanin bangaren gwamnati da dakarun ko ta kwana na rundunar RSF, ya sake dagula lamura a yankin na Darfur.

An dai dora laifi ne a kan 'yan tawaye masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Mohamad Hamdan Dagalo da ma wasu masu kama da su suka kaddamar.