Tarayyar Turai za ta kula da iyakokin Libiya
May 22, 2013Shugabannin Tarayyar Turai sun amince da tura wata tawagar jama'ai fararen hula da za ta riƙa kula da kan iyakokin ƙasar Libiya. Sanarwar ta ce jami'an wadanda za su fara aiki daga watan gobe, za su tallafawa gwamnatin Libiya domin ta iya kare iyakokinta da makobtanta, ta ruwa da sama da ta ƙasa, wanda tun bayan kifar da gwamnatin kanal Gaddafi, sabbin hukumomin ba su samu iko da daukacin iyakokin ƙasar ba. Kantomar kula da harkokin ƙetare ta kungiyar EU Catherine Ashton, tace dama wannan yana cikin tsarin bayan kammala yaƙin Libiya. Shirin wanda ake saran zai laƙume kudi har euro miliyan 30, zai hada da horar da jam'an shige da fice na kasar ta Libiya da kuma sanin makamar aiki, ta yadda za su kare iyakokin ƙasar dake fadin murabba'in kilo-mita 4,300, kana a gaɓar ruwa Libiya na da iyaka mai tsawon kilo-mita 2000, inda baƙin haure ke tsallakawa zuwa Turai.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Saleh Umar Saleh