1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Adolf Hitler

December 16, 2011

An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afirilu na shekara 1889, ya kashe kansa ranar 30 ga watan Afirilu na shekara 1945 bayan an ci Jamus da yaki

Hitler na jawabi a MajalisaHoto: picture-alliance/Imagno

An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 1889 wato shekaru 122 kenan da suka gabata.An aife shi a wani gari mai suna Braunau-am Inn, a kasar Austriya kusa da iyakar kasar da Jamus.Shine na hudu a gidansu.Mahaifinsa wani jami'in Custum ne,ya rasu a yayin da Hitler ke da shekaru 14 da aihuwa.

Marubuta tarihin Hilter sun ce bai yi wani dogon karatu ba, ya yi wasti da makaranta a lokacin da ya ke dan shekaru 16 da aihuwa.

Yayi yarintarsa cikin matsaloli masu yawa.Ya na samun 'yan kudaden tallafi da gwamnati ke baiwa marayu, sannan kuma ya na sana'ar zane-zane da kera-keren hannu.Saidai duk da cewar bai yi wani dogon karatu b,a mutum ne mai shawar karance-karance, kuma a wani lokacin har ma ya kan je ya saurari mahaurori a majalisar dokokin Austriya.

Saidai kuma tun ya na dan samari ya ke  nuna kyamar tsarin mulkin demokradiya da tsarin kominisanci.

Zuwan Hitler Jamus:

Adolf HitlerHoto: picture-alliance/dpa

Adolf Hitler ya zo Jamus a shekara 1913, ya gudo daga Austriya domin gudun kar a dauke shi cikin rundunar soja da kasar. Ya zauna a birnin Munich na jihar Bavariya.

Ya na nan ne yakin duniya na farko ya barke a shekara 1914.

Hitler ya shiga rundunar Jamus  a matsayin sojan sa kai,kuma ya nuna hazaka da jarumtaka  kwarai a cikin harkokin soja, saboda haka ne ma ya samu lambar yabo ta mussamman daga manyan sojojin kasar.A lokacin yakin duniyar, ya samu raunuka har so biyu wanda cilas aka kwantar da shi asibiti.A karshen yakin ya samu galar Caporal.

Bayan barkewar wani juyin juya hali a Munich, hukumomi sun kafa komiti wanda aka dorawa yaunin binciko gaskiyar al´amarin da ya faru.Hitler ya na daga cikin membobin wannan komiti kuma ya nuna basira kwarai ta fannin jawabin gaban jama´a.

Mussaman ya shahara wajen fasa wuta kokuma yafa mata ruwa ta hanyar kalamomin baki.

Wannan baiwa ta bashi farin jini kwarai daga mutane.

A fannin siyasa ya shiga wata karamar jam'iya mai suna DAP wadda ta kunshi ma´aikata zalla masu tsantsar akidar kishin kasa,wadda ta rikida zuwa NSDAP .Ya karbi jagorancin wannan jam'iya a shekara 1921.Ta wannan hanya ce ya fara yada akidarsa ta Nazi.

Kasancewar sa mutum da ya shahara wajen magana, sai ya zama daya daga jigajigen 'yan siyasa a jihar Bavariya.Sabo da karfin fada a ji da ya fara samu, ya jaraba yin juyin mulki a birnin Munich a shekara 1923 amma ba yi nasara ba.

An cafke shi, kuma a ka zartar masa da hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku, to saidai maimakon haka watani tara kawai yayi daure domin daga baya ya samu afuwa.Yayi amfani da wannan dama ta zama gidan yari,inda ya rubuta wani littafi mai suna da jamusancin "Mein Kampf", idan aka fasara da hausa, ya na nufi yakina, wato ma'ana a cikin wannan littafi ya bayyana dalla-dalla manufofinsa da akidojinsa.

A cikin manufofin Hilte,r ya bayana shawa ga akidar nan ta wani masani mai suna Darwin game da fadi tashin rayuwa.

Hitler ya bada fifiko ga wata kabilar Jamus mai suna Aryenne wadda akwaita a kasashe da dama na yankin arewancin Turai.A tunanin Hitler duk sauran kabilu na matsayin bayi ga kabilar ariyawan Jamus, wadda yace itace kabilar da ta fi daukaka a duniya, kuma itace ta kamata ta mulki duniya gaba daya.Hitler yayi mummunar suka ga yahudawa wanda ya dangata da annoba  a cikin rayuwa duniya saboda haka nema a lokacin yakin duniya na biyu ya sa aka hallaka miliyoyin yahudawa.

A cikin wannan littafi na yakina Hitler ya bayyana aniyarsa ta mamaye duniya

A wani abu mai kama da faduwa tayi daidai da zama,lokacin Jamus da sauran kasashen Turai,sun fara tsunduma cikin wata matsalar kariyar tattalin arziki.Ta la'kari da fadakarwa da Hitler ya tsananta yi ,sai jam'iyarsa ta NSDAP  ta kara samun karbuwar daga jama'a.

Sannu a hankali magoya bayan wannan jam´ iya suka fara daukar shi a matsasyin wani abin bautama.

A zaben da aka shirya a shekara 1930 jam'iyar ta samu kujeru.

Wannan babban  cigaba ya sa cilas shugaban kasar Jamus na wacen lokaci Mashal Hindenburg ya nada Hitler a matsayin shugaban gwamnatin Jamus ranar 30 ga watan Janairu na shekara 1933.

Hitler ya shimfida mulkin kama karya, ya kuma haddasa barkewar yakin duniya na biyu:

Hermann Göring(tsakiya) da Rudolf Heß (dama)mukkaraban Hitler lokacin yakin duniya na biyu sun gurfana gaban kotu.Hoto: picture-alliance/dpa

 Wata daya bayan da Hitler ya kama shugabancin gwamnati sai majalisar dokoki ta yi gobara.

Hitler sai ya dora alhakin gobara ga Marinus Van der Lubbe wani jigo a jam'yar 'yan communist wadda ya ke mummunar adawa da ita.Yayi amfani da wannan dama inda ya cafke dubunan magoyan bnayan wannan jam'iya.A washe garin wannan gobara sai shugaban kasar Jamus ya rattaba hannu kan dokar tabace wadda ta ba Hitler cikkaken mulki, sannan daga baya shugaban sake rattaba hannu kan wata sabuwar doka, wadda ta ba Hitler wuka da nama har tsawan shekaru hudu ya gudanaa da mulki ba tare da katsalandan din shugaban kasa ba.

Daga wannan lokaci ya fara cin karensa babu babbaka, ta hanyar shimfida mulkin kama karya.Ya soke jam'iyun siyasa da kungiyoyin kwadago, sannan yayi amfani da wannan dama domin kara yada manufofin jam'yarsa.

Shugaban kasar Jamus Hindenburg ya rasu ranar 12 ga watan Ogusta na shekara 1934.Adolf Hitler yayi gadon sa sannan kuma shi ke rike da matsayin shugaban gwamnati da kuma Führer wato shugaban jam'iyarsa.

Hakikanin gaskiya Adolf Hitler shi ne ya yi sanadiyar barkewar yakin duniya na biyu.

Tun lokacin da ya wallafa littafinsa mai suna Yakina ya bayyana manufofinsa na mamayar duniya.To kuma gashi dama ta samu, domin shine shugaban kasar Jamus kuma shugaban gwamnati.

A cikin burinsa na mamayar duniya,Hitler ya kuduri aniyar cimma wani buri da ya saka wanda aka fi sani da jamusanci da suna Anschluss:wato ya hade Jamus da  kasashen masu makwabtaka da ita kamar su Austriya da Chekoslobakiya.

Banda wannan kasashe ya aika dakarun Jamus domin mamaye kasashe kamar su Poland,Danmark,Beljima,da Faransa.

Mamayar kasar Poland daga nan ne yakin duniya na biyu ya barke, bayan da

A dalili da hakan ne yakin duniya na biyu ya barke a shekara 1939.

An yi ta gwabza fada tsakanin dakarun Jamus da sauran sojojin kawance har zuwa shekara 1945, inda Jamus ta yi saranda.

Marubuta tarihin Hitler sun ce ya kashe kansa a cikin gidansa na karkashin kasa ranar 30 ga watan Afrilu na shekara 1945, amma akwai mahaura game da mutuwar tasa.

Wata ruwaya ta ce ba  a wannan rana ne Hitler ya mutu ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman