Tarihin Barack Obama
August 28, 2008
An aifi Barack Hussain Obama ranar 4 ga watan Oguster na shekara ta 1961 a birnin n Honolulu dake yankin Hawai a ƙasar Amurika.
Tun yana ɗan shekaru biyu da aihuwa iyayensa suka rabu, ya cigaba da zama tare da ma´aifiyarsa.
Ubansa musulmi ƙan kasar Kenya a nahiyar Afrika, ya bar Amurika bayan ya rabu da matarsa ba´amurika inda ya koma gida Kenya, ya kuma zama minister a cikin gwamnatin shugaban ƙasa na farko, wato Jomo Keniyatta, kamin Allah ya amshi ransa, a shekara ta 1982 a cikin haɗarin mota.
A lokacin da ya samu shekaru shida, har zuwa shekaru 10, Barack Obama ya bi ma´aifiyarsa a ƙasar Indonesia inda suka yi zama na shekaru huɗu.
Sai a shekara ta 1971 ya komo Honolulu, inda ya ci gaba da karatu.
Yayi karatu a jami´ar Californiya da kuma ta Columbiya a birnin New York.
Bayan ya kamalla karatu, a jami´a, Obama ya fara aiki a matsayin jami´i, ta fannin lissafin kudi.
To saidai ba jima ba yana wannan aiki ya kuma koma ƙarin ilimi, inda a shekara ta 1991 ya fito da digrin digirgir ta fannin sharia´a.
Barack ya jima ya na kwaɗayin shida siyasa, amma sai a shekara ta 1996 haƙƙarsa ta cimma ruwa, inda karon farko a ka zaɓe shi a matsayin dan majalisar a mazaɓarsa ta yankin Ilinois.
A shekara ta 2004 ya shiga Majalisar Dokokin Amurika.
A tsawan watani 18 Barack Obama na fafatawa da matar tsofan shugaban ƙasar Amurika, wato Hilary Clinton domin samun tabaraki daga jam´iyar Demokrate don tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurikar.
A wani matakin da wasu ke dangatawa da "rabbo rabbabe", babbu zato babu tammaha, Barack Obama ya kai gaci tare da kasa abikiyar hammayar tasa.
A duk tsawan wannan lokaci Obama ya bayyana kansa a matsayin gwarzo, duk da cewar da dama na masa zargin rashin ƙurrewa cikin harakokin siyasa, idan aka kwatanta shi da Hilary Clinton, ko kuma da ɗan takara jam´iyar Republicain John Makain, mai shekaru 72 a duniya,wanda kuma ya laƙanci ƙabli da ba´adin siyasa, a ciki da wajen Amurika.
Ta fannin rubuce rubuce,Barack Obama, ya rubuta littatafai guda biyu, inda a ɗaya daga cikin su, yayi tarihin rayuwar baƙƙaƙe a Amurika, tare da bayyana yadda a matsayinsa na baƙin ba´amurike ya gudanar da yarintarsa.
Barack Obama,na da aure da kuma ´yaya,´yan mata guda biyu.
Abinda Amurika da sauran al´umomin duniya suka zuba idio su gani a halin yanzu shine ko Amurika ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a duniya, za ta sami a karon farko cikin tarihi, shugaba baƙar fata ? Sai mu dakaci ranar 4 ga watan November na wannan shekara.