1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Champions League

May 29, 2012

An yi shekaru 57 da fara gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Turai wato Champions League

ARCHIV - Der Champions League-Pokal steht im Hauptquartier der UEFA in Nyon in der Schweiz (Archivfoto vom 23.06.2006). Die begehrteste Trophäe für europäische Fußball- Vereinsmannschaften ist bereits die fünfte Anfertigung. Die vier Vorgänger sind gemäß UEFA-Statut schon in Vereinsbesitz übergegangen. Nach insgesamt fünf Siegen oder drei Erfolgen hintereinander darf der Cup behalten werden. Das gelang bisher Real Madrid und dem AC Mailand als fünfmaligen Siegern sowie Bayern München und Ajax Amsterdam, die in den siebziger Jahren jeweils den Titel-Hattrick schafften. Foto: Salvatore Di Nolfi (zu dpa 0408 vom 24.08.2006) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Tarihin Champions League:

Hukumar dake kula da wasani kwallo a kasashen Turai wato UEFA ta kirkiro wasan kwallon kafa na Champions League ko kuma Ligue des Champions tun shekara 1955 wato yanzu shekaru 57 kenan da suka gabata kuma ana yi wannan wasa ko shekara kenan yanzu an yi gasa daya nan bindaya har 57.Da farko kungiyoyin kwallo 76 wanda suka fi kwazo a kasashe daban-daban na Turai ke shiga gasar, bayan anyi tankade da rauraya sai su koma 32 wanda sune za su fafata ya junansu, har a kai ga karon karshe, wanda zai tantance Club din da ya zama gwarzon shekara.

Wasu 'yan jaridar wasani dake birnin Paris na kasar Faransa suka fara bada sharawa kirkiro wasani kwallon da zai hada zakarun kungiyoyin kwallo na Turai, bayan tunai da nazari hukumar UEFA da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya cewa da FIFA suka bada izinin shirya wannan gasa karon farko a birjin Lisbonn na kasar Portugal gaban 'yan kallo fiye da dubu 30.An yi karon farko ranar hudu ga watan Satumba na shekara 1955 tsakanin le club din le sporting na Portugal da Partizan Belgrade na Yougoslaviya, an tashi kunnen doki ukku da ukku.A wannan karo na farko an buda wasan karshe tsakanin Real Madrid ta Spain da Stade de Rheims na kasar Faransa, inda a ka tashi 4 da uku watoi Real Madrid ta samu nasara zama club din farko da ya lashe gasar kwallon kafar kasashen Turai.

kungiyoyin kwallo da suka taba yin nasarar zama zakaru tun daga na farko a shekara 1955 har zuwa yanzu.

Real Madrid ita ke sahun gaba daya na bin daya ta yi nasara zama zakara har sau tara.Saida ta jera shekaru biyar daya daga farkon wasan har zuwa 1960 ta samun kofi, sannan ta ci a shekara 1966 da 1998, 2000 da kuma 2002.banda haka ta yi wasan karshe gaur sau uku inda b a ta samu nasara ba.

Bayan Real sai AC Milan ta kasar Italiya wadda ta ci wannan kofi sau bakwai sannan kuma ta yi wasan karshe so 4 ba tare da samun nasara ba.

Club na uku ta fannin cin kofi a wasanin Champions League shine Liverpool FC na Ingila wanda ya samu kofi sio biyar kuma ya buga wasan kasrhe so biuy bai ci nasara ba.

A sahu na hudu akwai Bayer Munich na kasar Jamus wana ya vi kofi so hudu kuma ya buda wasan karshe so biyar ba tare da nasara ba, na biyar shine FC Barcelona wanda ya dauki kolfi so 4 kuma ya buga wasan karshe so uku ba tare da samun nasara ba.

Shima club dinAjax na Amsterdam ya dauki kofi so hudu saidai ya buga wasan karshe biuy ba tare da nasara ba.

Manchester United da Inter Milan na matsayi guda, ko wane daga cikinsu ya dauki kofi so uku, kuma ya buga wasan karshe bai ci nasara ba so biyu.

A atsayi na tara akwai Benfica Liasbon da kuma Juventus FC wanda ko wane daga cikin ya dauki kofi so biyu, kuma ya buga wasan karhse bai yi nasara ba so biyar.

Akwai FC Porto da kuma Nottingham Forest FC ko wane ya dauki kofi sa biyu.

Sannan akwai wasu kungiyoyin kwallo guda 10 wanda suka taba daukar kolfi so daya sune: Celtic Glasgow, Hambourg SV, Steau Bucarest , Olympic ta Marseille,Feyenood Rotterdam,Aston Vila FC,PSV Eindhoven, Etoile Rouge de Belgrade Borussia Dortmund sai kuma Chelsea wadda itama a karon farko ta lashe wannan kofi a wasan shekara bana.

Sannan kuma kawai kungiyoyin kwallon da dama wanda sun taba yin karo karskhe amma ba su yi nasara lashe kofi ba misali akwai Valence FC, Stade de Rheims, AS sint Etienne Atletico ta Madrid Borussia Mönchengladbach,AS Roma, AS Monaco,Arsenal FC, Bayer Leverkusen da dai sauran su.

Idan aka bi ta fannin kasashe, kasar ta fi sauran daukar kofin gasar cin kwallon kafa ta kasashen Turai, domin Spain ta dauka har sau 13 kuma ta yi karon karshe da ba ta samu nasara ba so tara, ta biyu itace kasar Italie wadda ta cin kofin har so 12 sannan ta yi karon karshe wato final so 14 wanda ba ta yi nasara ba.

Raul GonzalesHoto: Reuters

Sai ta ukku itace kasar Ingila wadda ta vdauki kofi 12 amma ta yi karon karshe so bakwai wanda ba ta yi nasar ba.

Jamus ke matsayi na hudu, domin ta dauki kofi so shida ta je matakinfinal so tara ba tare da nasara ba.

Itama Holland ta dauki kofi so shida amma so biyu kawai ta taba yin karon karshe wanda ba ta yi nasara ba.

Portugal ta ci wannan gasa so hudu, Faransa ta ci so daya tilo amma ta je final har so biyar ba ta yi nasara ba.

Kasashen Scotland, Roumaniya Yougoslaviya ko wace ta ci so daya kuma ta yi karon karshe so daya wanda ba ta yi nasara ba.Sannan akwai kasashe Girka,Beljiam da Sweedin wanda sun ta ba yi karon karshe so guda-guda, amma ba su taba yin nasara samun kofi ba.

'Yan wasan da su ka fi shahara a cikin shekaru 57 na Champions League ta fannin zura kwallo raga.

Hoto: dapd

Idan muka dauki tarihin wannan gasa daga farkon ta har zuwa shekara bana, wato 2012, tarihin ya nuna cewar dan wasan da ya fi sauran yawan zura kwallo raga shine Raul Gonzalez wanda yayi buga wasa a Real Madrid da kuma Schalke 04 ta nan Jamus a jimilce ya yi buga wasa har sau 144 wanda a cikin su ya zura kwallo har so 71.

Na biyunsa shine Andry Shevchenko wanda ya wasa a Dynamo Kiev da AC Milan da kuma Chelsea FC ya zura kwallaye 59 raga, sannan akwai Ryan Giggs na Manchester United wanda ya saka kwallo har so 30 a cikin wasani daban-daban na Champions League.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal