Tarihin John Atta Mills
July 30, 2012
John Evans Fifii Atta Mills da wasu kewa laƙabi da suna Prof wato Profesa kenan an haife shi ranar 21 ga watan Juli na shekara 1944 wato shekaru ya na da shekaru 68 kenan daidai a duniya Allah ya karɓi ransa.An haife shi a wani gari da ake kira Tarkwa da ke yammacin ƙasar Ghana.Yayi karatu amakarantar Achitoma School inda ya swamu digirin farko a shekara 1963, kamin daga bisani ya shiga jami'ar Legon ta ƙasar Ghana, inda ya yi karatu ta fannin shari'a.
Bayan jami'ar Ghana ya ci gaba da neman ilimi a ƙasar Birtaniya inda ya yi karatu a wata makarantar tattalin arziki da hallayar ɗan Adam, bugu da ƙari yayi karatu a jami'ar London, inda ya samu digirin digir-digir ta fannin shari'a da kuma husa'a cigaban tattalin arziki.
Bayan ya dawo gida Ghana ya fara koyarwa a sashen shari'a na jami'ar Ghana, inda ya share kusan shekaru 25 ya koyar da ɗallibai.
A shekara 1971 ya samu nasar zuwa ƙarin ilimin a ƙasar Amurika a wata makaranta da ake kira Stanford Law School.
Tsakanin shekara 1978 da 1979 da kuma tsakanin shekara 1986 zuwa 1987, Pr John Atta Mills ya yi zaman koyarwa a wata makaranta mai suna Temple Law School da ke Philadelphie a ƙasar Amurika.Sannan daga shekara 1985 zuwa 1986 ya kokoyar a wata jami'a mai suna Leiden Uuiversity daka ƙasar Holland.
A tsukin wannan lokaci ya rubuta littatafai da dama ta fannin shari'a, tattalin arziki da haraji.Saboda ƙurewarsa ta fannin shari'a da haraji gwamnatin ƙasar Ghana tanada shi mataimakin babban darakta mai kula da hukumar haraji ta ƙasa daga shekara 1986 zuwa 1993 kamin daga bisani ya samu shugabancin wannan hukuma na tsawan shekaru uku wato daga 1993 zuwa 1996
Lokacin da Parfesa John Atta Mills ya shiga harkokin
Pr.John Atta Mills ya shiga harkokinsiyasa gadan-gadan tun lokacin da shugaban ƙasa John Jerry Rawlings ya naɗa shi mataimakinsa, matsayin da ya riƙe daga shekara 1997 har zuwa, 2000 wato shekaru uku kenan ya na riƙe da matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Bayan da Jerry ya kamalla wa'adin mulkinsa, sai jam'iyar NDC ta tsaida John Atta Mills a matsasyin ɗan takarara ta a zaɓen shekara ta 2000,inda ya fafata da dan takara jam'iyar NPP mai adawa a lokacin wato John Kuffor.A zagayen farko John Atta Mills ya samu kashi 44,8 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a yayin dan abokin hammayarsa John Kuffor ya samu kashi 48 cikin ɗari, cilas kenan aka tafi zagaye na biyu, wanda sakamakon sa, ɗan takara adawa John Kuffor ya lashe zaɓe.
A watan Disemba na shekara 2002 jam'iyar NDC ta sake tsaida John Atta Mills a matsayin ɗan takararta a zaɓe shugaban ƙasa da Ghana zata shiryawa a shekata ta 2004, a wannan zaɓe kuma karo na biyu John Atta Mills ya sha ƙasa.To amma hausawa ke cewa wai mahaƙurci mawadaci, a wata Desemba na shekara 2006 NDC ba ta dadara ba ta sake tsaida shji a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasar da za a iya a shekara 2008, to a wannan karo ne ya ɗauki fansa.
Ya fafata tare ɗan takara jam'iyar NPP mai mulki wato Nana Akufo Addo domin shi John Kufor ya kammalla wa'adin mulkin guda biyu na shekaru huɗu -huɗu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, saboda haka bai tsaya takara ba.An ce wai duniya rawar 'yan mata na gaba ya koma baya, a wannan karo sai John Atta Mills ya yi nasara lashe zaɓe da kashi 50,23 na ƙuri'un da aka kaɗa,kenan dan takara jam' iya mai mulki ya sha kayi.
Nan da watani huɗu kacal ta kamata Ghana ta shirya zaɓen shugaban ƙasa kuma tuni har jam'iyar NDC ta tsaidai John Atta Mills a matsayin ɗan takararta, to amma kana taka Allah na tashi,a cikin wannan yanayi ne na yaƙin neman zaɓe Allah ya karɓi ran John Atta Mills ranar 24 ga watan Juli na shekara 2012, a asibitin sojoji ta birnin Accra.
Rashin lafiyar John Atta Mills
Haƙiƙa cemma al'umar ƙasar Ghana, ta san da cewar shugaba John Atta Mills ba shi da ƙoshin lafiya to amma babu wanda yayi zaton rashin lafiyar ta kai matsayin da ta kai
Marigayi John Atta Mills na samu kyakkyawan yabo d addu'o'in alheri daga sassa daban-daban na duniya game da aiyukan alheri da ya yi ga al'umar ƙasar Ghana kamin Allah ya karɓi ransa.
John Atta Mills ma'abuci ne nkwarai na wasan gora, ya na daga cikin membobin ƙungiyar masu wasan gora ta ƙasa da suka yi ritaya har lokacin da Allah ya karɓi ransa.
A ɗaya hannun ya na shawara iwo cikin ruwa domin wanda ke zaune tare da shi ,sun ce kusan kullum sai ya yi awa biyu cikin ruwa, wato irin dan tafkin nan na ruwa na zamani wanda ake gani a gidajen hotel ko kuma gidajen masu hannu da shuni.
Bangaren wasani ƙwallon ƙafa kuwa suma ya na shawar su domin kamar da dama daga ma'abuta ƙwallon ƙafa a Afrika ya na kallon wasani ƙwallo na ƙasashen Turai,ƙungiyar ƙwallo ta Manchester United ita ya ke goya wa baya.
Ta ɓangaren iyali John Atta Mills ya na mata guda mai suna Ernestina Naadu Mills, suna da ɗa guda sunansa Sam Kofi Atta Mills.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammed Abubakar