1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin kasar Libiya

February 21, 2012

Libiya mai yawan mutane miliyan bakwai ta samu 'yancin kanta a shekara 1951

Karte Libyen Provinzen Tripolitania, Cyrenaica, Fezzan DW-Grafik: Olof Pock Libyen.jpg

Libiya kasa ce dake yankin arewacin Afrika, tana makwaftaka da da tekun Bahrum a bangaren arewa, daga yamma ta na iyaka da kasar Aljeriya da Tunisiya a kudancinta ta yi iyaka da Jamhuriya Nijar da Chadi sai kuma a sashen yamma ta yi iyaka da kasashen Sudan da Masar.Ta fannin girman kasa, itace kasa ta hudu a Afrika, sai dai ba ta yawan mutane sosai, domin dududu al'umar kasar ba su wuce miliyan bakwai ba.

Game da mulkin mallaka idan mu ka shiga cikin tarihi mai nisa kasashen Girka da kuma romawa na Italiya sunyi wa Libiya mulkin malka yau shekaru kusan dubu daya da dari biyar.

A shekara ta 641 wato shekaru kusan 1400 su kuma suma larabawa yan kabilar Aghlabide sannan 'yan Fatimide, suka kutsa Libiya suka mallake ta a lokacin da suke gwagwarmayar yada addinin musulunci,Kamin daga bisani kasar Spain ta kwace birnin Tripoli a shekara 1510.

Sannan shekaru 40 bayan an sai sarkin Daular Ottamaniya na wannan lokaci wani mai suna Suleiman ya kwato Libiya da Tripoli daga hannun Spaniyawa.Libiya ta kasance cikin mulkin mallakar Turkiyya har shekara 1911 wato shekaru 100 kenan da suka gabata inda kasar Italie ta yi nasara kan Mustafa Kemal na Turkiyya kuma ta kwace Libiya daga hannun turkawa.Italiya ta yi mulkin Libiya har zuwa shekara 1943 wato shekaru kusan 70 kenan da suka shude.

A wannan lokaci ne na yakin duniya na biyu inda hadin gwiwar sojojin Faransa da na Ingila, suka yi wa Italie taron dangi a Libiya suka kore ta daga yankin gaba daya.

Bayan da suka ci yakin Libiya sai Faransa da Birtaniya suka raba Libiya, Birtaniya ta dauki yakunan Tripolitaine da Cyrenaique, a yayin da Faransa ta dauki yankin Fezzan.

Ranar 21 ga watan Nowemba na shekara 1949 Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri´ a game da sake hade kasar Libiya wuri guda,hakan ya ba kasar Libiya damar samun 'yancin kanta ranar 24 ga watan Desemba na shekara 1951 wato yanzu shekaru 61 kenan kuma itace kasar farko a yankin Magreb da ta samu yanci daga turawa.

Shugaban kasar Libiya na farko bayan samun 'yancin kai:

Shugaban darikar sanussiya wato Sidi Muhamad Idriss al-Mahdi al-Sanoussi bugu da kari shugaban yankin Cyrenaique zamanin da kasar ta rabu tsakanin Faransa da Birtaniya shine ya zama shugaban haddadiyar kasar Libiya, ya dauki sunan sarki Idriss na daya.

Hoto: picture alliance/dpa

Kasar Libiya ta zama memba a Majalisar Dinkin Duniya a shekara 1955, kuma shekara daya bayan hakan aka gano rijiyar man fetur ta farjko a cikin kasar, wanda shugabanin suka yi amfani da shi domin gina wannan kasa.

A shekara 1969 Muhammar Khadafi a lokacin ya na dan shekaru 27 da aihuwa ya kifar da mulkin Sarki Idriss na daya.Tun daga wannan shekara Khadafi ya ci gaba da mulkin Libiya har shekara 2011 inda guguwar juyin juya halin da ta kada kasashen larabawa ta kifar da mulkinsa kuma 'yan tawayen suka hallaka shi.

Ba za mu dawowa ba bisa tarihin mulkin Muhamar Khadafi domin mun sha bada wannan tarihi a cikin shirye shiryenmu na baya.

A yanzu dai 'yan tawayen da suka kifgar da mulkinsun girka wani komitin rikwan kwarya bisa jagorancin Mustapaha Abdel Jalil da kuma Abdel Rahim Al-Kib a matsayin Firaminisitan rikwan kwarya kamin shirya zabe a cikin wannan shekara.

Arzikin man fetur a Libiya:

Babu shakka tamakar Libiya man fetur, a Afrika itace kasa ta biyu bayan tarayya Najeriya game da albarkatun man fetur.To amma ta fannin man fetur na rumbun tsimi ta tserewa Najeriya.A shekara da ta gabata an kiyasta yawan man fetur din da ke kwace karkashin kasa a matsayin na tsimi,har ganga miliyan dubu 46 da rabi.

sabuwar tutar Libiya

Man fetru na samar da kashi 93 cikin dari na kudaden dake shiga aljihun gwamnatin Libiya sannan man fetur na matsayin kashi 95 cikin na hajojin da Libiya ke fidawa a kasashen ketare

Banda man fetur, ana sayar da albarkatun noma zuwa kasashen ketare ko da shike ma dai a kashi daya ne cikin goma na filin kasar ake yin noma.Kamfanoni da masana'antun da kasar ibiya ta mallaka sun hada da kamfanonin sarrafa albarkatun noma sai kuma na saka sune suka fi yawa a kasar, akwai kuma kamfanonin samar da siminti da dai wasu wanda ba su cika yawa ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal