1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin mallakar makamai masu Guba a Siriya

July 26, 2012

Hukumomin leken asirin ƙasashen yammaci na turai sun ruwaito cewa sojojin gwamnatin Assad sun kwaso wasu makamai masu guba daga wurin da ake ajiyarsu.

In this image made from amateur video released by the Ugarit News and accessed Monday, July 23, 2012, Free Syrian Army soldiers sit on a military tank during clashes with Syrian government troops in Aleppo, Syria. The Syrian regime acknowledged for the first time Monday that it possessed stockpiles of chemical and biological weapons and said it will only use them in case of a foreign attack and never internally against its own citizens. (Foto:Ugarit News via AP video/AP/dapd) TV OUT, THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Hoto: AP

Wannan yunƙuri dai ya haifar da tsoro dangane da yiwuwar amfani da su wajen kai hari akan 'yan adawar ƙasar dake bore. Sai dai ministan harkokin wajen Siriyar ya tabbatar da cewar, gwamnati ba ta da niyyar amfani da su akan al'ummar ƙasar, sai dai idan har an kawo musu hari daga ketare.

Tun a shekarun 1970s ne dai Siriya ta mallaki makamai masu guba. Ƙasar ta fara sarrafa makamai masu guba ne gabannin yaƙin Jom-Kippur da ta yi da Izraela a shekara ta 1973. Tun daga wancan lokacin ne dai Siriya tare da tallafin tsohuwar tarayyar Soviet, kana daga baya Iran ta rika tallafa mata wajen sarrafa irin waɗannan makaman. Kazalika ta kuma samu tallafin kammala sarrafa su da taimakon wasu kampanonin ƙasashen Turai da suka haɗar da Jamus.

A yanzu haka dai ƙasar ta Siriya na mallakar ɗaruruwan ton-ton na makamai masu guba da aka jibge su a wurare daban-daban. Ma'ajiyar dai suna birane huɗu da suka haɗar da Damaskus, Aleppo, Homs da Hama. Sai dai ana zargin cewar akwai ƙarin wasu a wasu sassan ƙasar da ba'a sani ba. Sai dai sun kasance ƙanana ne kuma, yana da wuya a iya gane su. Kazalika akwai zargin cewar sojojin Siriyar na mallakar makamai masu linzami kamar na SS-21 irin na Rasha da koriya ta arewa, da rokoki waɗanda za'a iya amfani dasu da makamai masu guban. Da waɗannan makamai dai ana iya kai hari har zuwa nisan km 600.

Jihad MakdissiHoto: Reuters

Shakkun manazarta akan yiwuwar amfani da makamai masu guba

To sai dai a cewar Dina Esfandiary dake cibiyar nazarin al'amuran ƙasa da ƙasa, yana da wuya Assad ya yi amfani da waɗannan makamai akan al'ummarsa...

Tace" yana da matuƙar wuya ace Assad da gwamnatinsa suyi amfani da makamai masu guba akan jama'arsa ko kuma dakarun ƙasasahen waje, kamar yadda aka yi nuni dashi 'yan kwanakin da suka gabata. Kasancewar lokaci kalilan ya rage wa Assad, yin amfani da waɗannan makami masu guba na tabbatar da cewar ƙarshensa ya zo, domin hakan zai saɓawa ƙasashen yammaci, kuma saɓa musu tamkar yana rattaba hannu ne a takardar mutuwarsa".

Esfandiary ta yi nuni da cewar hukumomin leken asirin turan na sane da ɓangaren shirin makamai masu guban na Siriya a fakaice. Sai dai a zarginta, ba su da masaniya dangane da shi shirin bakin ɗayansa. Hakan ne kuma zai kasance abu mawuyaci su iya samarwa da al'ummar Siriyan irin kariya da suke bukata, ballantana kare makaman daga shiga hannun ƙungiyoyin tarzoma na ƙasar.

Ta ce " akwai takaitaccen irin amfani da za'a iya yi da makamai masu guba. Ba makamai ne da ake amfani dasu a fagen daga, ko makaman yaƙi, suna da wahalar amfani dasu, kasancewar suna dogaro ne da iska da kuma inda zasu sauka. Sai dai wadannan makamai ne na ta'adanci, domin za'a iya amfani dasu wajen da mutane suke, wajen tsoratarwa, a wannan yanayi suna tasiri".

Hoto: AP

Kazalika mai bincike a cibiyar nazarin harkokin tsaro a Tel Aviv Schlom Brom, yana da ra'ayin cewar makaman nada wahalar kulawa dasu. Musamman idan suka kasance a wurare daban daban na ajiya...

Yace " kafin ka yi amfani da wadannan makamai masu guba, ya zamanto wajibi kana da cikakken masaniya akansu, dama ma hanya mafi dacewa na yin sufurinsu, dalili kenan da ya sa zai kasance abu mawuyaci ace gungun mutane kalilan su iya kulawa da dukkanshi, sai dai ɓangare guda kawai".

A yanzu haka dai al'ummar ƙasar ta Siriya na cikin fargabara yiwuwar, shugaba Basha al-assad yayi amfani da waɗannan makamai masu guba akansu, idan ya ga cewar bashi da wata mafita na rugujewar gwamnatinsa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal