Tarihin mawaƙi Abubakar Ladan Zariya
August 2, 2010Talla
An haifi Alhaji Abubakar Ladan Zariya ne a shekarar 1935 a Anguwar ƙwarbai dake birnin Zariya a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya. Bayan shekara biyar da haihuwan sa an saka shi a makarantar Allo. Bayan ya sauke karatun Qur'ani a shekarar 1946, ya shiga makarantar share fagen shiga Elementare in da kuma ya kammala a 1950. Daga nan kuma ya shiga makarantar middle ta Zariya da ake kira Alhudahuda. A shekarar 1954 Abubakar Ladan ya kammala makarantar Alhudahuda, sai kuma ya fara aiki a garin Malumfashi. Daga nan kuma ya fara aikin malamin dabbobi ko vetanariya, inda yake fannin bincike akan ƙudan tsando. Bayan ya bar aikin vetanariya, ya kuma fara aiki a matsayin malamin kula da ingancin fatu da ake sasarafawa a kanfanoni a Kano. Alhaji Abubakar Ladan ya fara waƙen Hausa ne a lokacin da ya fara karance-karancen waƙoƙin Hausa irin nasu Sa'adu Zungur da Mu'azu Haɗeja da kuma wani mawakin Larabci na Sudan mai suna Abdulkarem Al-ƙabirun. Abubakar Ladan ya kai ziyara ƙasashen Afirka da dama da suka haɗa da Sudan da Maroko da Habasha da Somaliya da su Kwango da Nijer da Iritiriya. Yanzu haka dai Alhaji Abubakar Ladan Zariya yana da 'ya'ya goma da kuma matan aure. A zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari an ba shi lambar yabo ta OFR. Mawallafi: Babangida Jibril Edita: Umaru Aliyu
Talla