1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Nana Akufo-Addo zababben shugaban Ghana

December 10, 2016

Hakar Nana Akufo-Addo ta cimma ruwa domin ya lashe zaben shugaban kasar Ghana bayan takara ta uku. Amma al'ummar Ghana na fatan cewa dan shekara 72 da haihuwar zai farfado da tattalin arziki tare da kirkiro aikin yi.

Ghana oppositioneller Kandidat Nana Akufo-Addo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A wani abin da aka dauka a matsayin damarsa ta karshe ta samun kujerar shugabancin kasar Ghana, hankoron samun canji tsakanin akasarin 'yan kasar Ghana ya taimaka Nana Akufo-Addo ya samu shiga fadar shugaban kasa. Bayan tsayawa takara sau biyu bai yi nasara ba, dan siyasar mai shekaru 72 ya kada shugaba mai ci John Mahama don jan ragamar mulkin kasar ta Ghana da mahaifinsa ya mulketa daga 1970 zuwa 1972.

A haifeshi ne a jihar gabacin kasar kuma yana da dangantaka da mutane ne uku daga cikin shida da ake wa lakabi da "The Big Six" da suka taka rawa wajen kwato wa Ghana 'yancinta daga turawan Ingila. Ya yi karatun sakandare a wata makarantar sakandare ta 'yan gatta da ke Birtaniya, sannan ya yi wani bangare na karatun jami'a a Kwalejin Oxford duk dai a Birtaniyar.

A yakin neman zabe a baya ya yi kokarin shawo kan mutane ne don wanke kansa daga zargin da ake masa na mutum mai girman kai, kamar yadda Burkhardt Hellemann na gidauniyar Jamus ta Konrad Adenauer reshen kasar Ghana ya yi karin haske.  

Nana Akufo-Addo ya samu hadin kan 'yan Ghana a wannan karonHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Ya ce: "Matsalar da Akufo-Addo ya fuskanta ita ce a zabukan 2008 da 2012 an yi masa kallon wani masani mai girman kai. Saboda haka ya sha da kyar wajen yin hulda da 'yan kasa."

 

'Yan Ghana na jiran sauyi daga Akufo-Addo

Zargin da Akufo-Addo ya yi cewa ya fadi a zaben 2012 ne saboda magudi da aringizon kuri'u bai yi wa da yawa daga cikin 'yan kasar har ma da wasu 'ya'yan jam'iyyarsa ta NPP dadi ba, bayan da babar kotun kasar da kuma masu sanya ido a zabe suka yi watsi da zargi. A karshe ya amince da hukuncin kotun kolin kasar na tabbatar da nasara da John Mahama ya samu.

A yakin neman zaben wannan shekara, an yarda da alkawuran da Akufo-Addo ya dauka domin masu zabe sun gaji da matsalar koma bayan tattalin arziki da makamashi da kuma batun cin hanci da rashawa. Clement Adjei fada ne kuma mai sa ido ne a zabe.

Ya ce: "Alkawuran da ya yi da hangensa sun fi samun karbuwa wurin jama'a. Idan ka duba yanayin da ake ciki za ka ga cewa mutane na neman canji saboda wahalhalun da 'yan Ghana ke sha."

 

Wa'adi daya na mulki Akufo-Addo zai yi

Akufo-Addo ya yi yakin neman zabe kan jerin alkawuran daidaita tattalain arziki da samar da guraben aiki kamar yadda ya fada wa tashar DW kwana guda gabaninn gudanar da zaben.  

Nana Akufo-Addo ya taba rike mukamin ministan harkokin wajen GhanaHoto: imago/Xinhua

Ya ce: "Za mu kirkiro guraben aikin yi kamar yadda ake yi a ko ina cikin duniya. Za mu farfado da tattalin arziki  za mu dauki matakan da za su samar da haka. Za mu karfafa kamfanonin Ghana na gwamnati da na masu zaman kansu. Mun yi amanna shi ne hanyar kirkiro da aiki mun kuma yi amanna za mu iya yin haka cikin gajeren lokaci."

A cikin watan janerun 2017 za a rantsar da Nana Akufo-Addo a matsayinn shugaban kasar Ghana. Sai dai ba a sani ba ko zai iya sake tsayawa takara don neman wa'adin mulki na biyu a 2020 saboda yawan shekaru domin a lokacin zai samu shekaru 76 a duniya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani