Tarihin sabon shugaban kasar Benin
April 14, 2016Talon ya kasance mai goyon bayan shugaban kasar da ya gabata watau Thomas Boni Yayi, saboda shi ya dauki nauyin yakin neman zabensa a shekarun 2006 da 2011.
Sai dai sabani ya shiga tsakanin mutanen biyu, sakamakon zargin da aka yiwa Talon na hannu a yunkurin kisan gillar shuga Boyi Yayi, zargin da ya sa ya gudu daga Benin din zuwa Faransa domin neman mafaka a shekara ta 2012. A shekarata 2014 ne aka yi masa afuwa.
A zaben shugaban kasa da ya gudana a watan Maris da ya gabatana wannan shekata ta 2016, Talon ya yi takara a matsayin dan takara mai zaman kansa. Duk da cewar ya zo na biyu bayana fraiminista Lionel Zinsou da suka yi takara tare a zagayen farko, hamshakin dan kasuwar audugar ya yi nasarar lashe zaben a zagaye na biyu da yawan kuri'u 65 daga cikin 100.
Patrice Talon ya na da aure da 'ya'ya guda biyu. Kuma a ranar Talata 6 ga watan Afrilu ne aka rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar ta Benin da ke yankin yammacin Afirka, a babban filin wasan kwallon kafa na Charles Degaulle na Porto Novo da ke a kudancin kasar da misalin karfe goma na safe, a gaban wakilai na jam'iyyun siyasa da jami'an diploamasiya na kasashen waje da kuma sarakunan gargajiya.