1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin shugaba Macky Sall na Senegal

April 3, 2012

Macky Sall mai shekaru 51 ya riƙe manyan muƙamai na gwamnati kafin ya zama shugaban ƙasar Senegal na huɗu. Ya na da mace ɗaya da kuma 'yaya uku.

Senegalese opposition presidential candidate Macky Sall speaks at a celebratory news conference in the capital Dakar March 25, 2012. Senegal's long-serving leader Abdoulaye Wade admitted defeat in the presidential election, congratulating his rival Sall, a move seen as bolstering the West African state's democratic credentials in a region fraught with political chaos. REUTERS/Joe Penney (SENEGAL - Tags: POLITICS ELECTIONS PROFILE)
Ƙarƙashin lemar APR Macky Sall ya zama shugaban Senegal.Hoto: REUTERS

An haifi Macky Sall an haife ranar 11 ga watan satumba ta shekarar 1961 a Fatick, wato garin da ya taɓa riƙe muƙamin magajin gari. Sabon shugaban na Senegal ɗan talakawa ne gaba da baya, domin kuwa mahaifiyarsa mai suna Coumba Thimbo geɗa ta riƙa sayarwa, yayin da mahinyasa Amadou Abdoul Sall ya yi aikin akawu a wata ma'aikata ta gwamnati kafin daga bisani, ya zama gadi.

Sai dai kuma wannan hali bai hana Macky Sall karatu na firamare da kuma sekondare a garuruwan Fatick da kuma Kaolack ba, kafin ya wuce zuwa Dakar babban birnin Senegal domin ci gaba da neman ilimi. Hasali ma dai, bayan da ya sami shaidar kammala karatun injiniya a fannin bincike a ƙarƙashin ƙasa na Senegal, ya je Paris na Faransa domin zurfafa ilimi a wannan fanni na hako man fetur. Macky sall dai na da mace ɗaya da kuma 'yaya uku.

Lokacin da Macky sall na Senegal ya fara siyasa

Shi dai Injiniya Macky sall tun ya na sekondare ya fara ma'amalla da harkokin siysa. Alalhaƙiƙa ma dai ya taɓa rungumar ra'ayin siyasa na gurguzu, kafin daga bisani wato a shekarun 1980 ya shiga cikin jam'iyar PDS, wadda tsohon shugaba Abdoulaye wade ya kafata. Sai dai Macky Sall ya raba gari da ubangidan nasa a shekara ta 2008, sakamakon nema da ya yi ɗan shugaba wade, wato karim ya yi wa 'yan majalisa bayani game da yadda ya ke kashe kuɗin da aka ware wa hukuma musulunci ta Senegal da ya ke shugabanta.

Abboulaye wade ne ya haska Macky sall a fagen siyasa.Hoto: dapd

Amma a ranar 1 ga watan disemba ta 2008, injiniya Sall ya kafa jam'iyar APR, wacce ta lashe kujerun kanseloli a a garin sa Haihuwa, da wasu ƙananan hukokim 12 na Arewacin Senegal da kuma uku a kudancin ƙasar a zaɓen maris na 2009. Tun daga wannan lokacin ba burin da ya sa a gaba, wanda ya wuce zama shugaban ƙasar Senegal.

Muƙaman da Macky sall ya riƙe kafin zama shugaba

Macky sall ya taɓa zama shugaban kanfanin albarkatun fetur na Senegal. kana ya taɓa zama mai bai wa shugaba Abdoulaye wade shawara a fannin fetur da sauran arzikin ƙarkashin ƙasa. Daga bisani ma wato a mayun 2001, ya zama ministan makamashi da albarkatun ruwa. Hakazalika sabon shugaban na Senegal ya taɓa riƙe muƙamin ministan cikin gida, kafin daga bisani wade ya naɗa shi firaminista a ranar 21 ga watan afrilun 2004.

'yan Senegal na cike da buri game da shugabancin Sall.Hoto: REUTERS

To Amma ɓaraka da ta fara kunno kai tsakanin wade da sall, ya sa sabon shugaban senegal karkata zuwa ga majalisa inda aka zaɓe shi kakaki a ranar 20 ga watan junin 2007. A zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana ranar 25 ga watan maris 2012 kuwa, Macky sall ya yi nasarar cika burinshi inda ya zama shugaban ƙasa bisa tallafi wasu jam'iyaun adawa da suka marasa baya, ciki kuwa har da Shahararren mawaƙin nan wato Yousou N'dour.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh