Tarin matsaloli ga masu noman rani a Kano
April 13, 2016Noman rani sana'a ce da ta jima tana rufa wa manoma da masu sha'awar noman musamman ma na karkara asiri. Baya ga magance matsalar zaman kashe wando, da wannan sana'a ce talaka ke biyan sauran bukatun rayuwa. Sai dai a 'yan shekarun nan musamman ma a bana manoman ba su ji da dadi ba. Alhaji Nasiru Haruna Roni manomin rani ne da ya sami kansa a wasu daga cikin matsalolin da suka taso wa sana'ar a bana.
"Na farko kasuwa ta cushe. Na biyu mun zo a kan gaba, man fetur da za mu yi amfani da shi wajen ban ruwa ya yi tsada. Sai kuma bana muka ga wani iftila'i wanda ba mu saba gani ba. Kwari sai suka zo mana fiye da yadda muke tsammani. Yu idan kana noman kayan miya za ka ga a gonarka kusan duk kwana uku sai ka yi feshi."
Rashin jari mai yawa na kassara kananan manoma
A duk shekara kananan manoma sai sun nemi bashi suke noman saboda karancin jari, damar da idan ta kuskure to sai gyaran Allah kamar yadda Malam Hudu wanda karamin manomi ne ya sami wannan matsala.
"Rashin jari ya hana ban sa karas da wuri ba. Lokacin ana sayar da shi Naira dubu goma nawa lokacin bai zo ba. Daga baya kuma muka zo da namu muna sayarwa Naira dubu uku, dubu hudu, dubu biyu ma mun sayar. Da yawa muka yi asara. Bayan mun cire kuma muka mayar da albasa. Albasar ga ta nan ita ma irin da muka yafa duk zubar da shi muka yi, muna tsoron ka da ta zo ta yi araha. Ga shi harkar tumatir, ni barinsa ma na yi saboda na ga yana araha, na zo na bar shi ya bushe. Idan na kashe kudi da taki da ruwa ma ba zan mayar da kudin ba."
Wadannan matsaloli haka suke a ko ina, idan ban da matsalar man fetur da manoman da suke ban ruwa da rijiya irin su Malam Hudu suka fi saura ji a jika kamar yadda ya saba yi.
"Fetur inji na zukowa sai ka kashe gallon daya gallon biyu gallon duk sati ka kashe gallon uku. Nawa za ka samu kuma nawa za ka kashe?"
Manoma na guje wa sana'ar saboda matsaloli
Wadannan matsaloli ne kuwa kamar yadda Alhaji Nasiru ya bayyana suka sa manoman rani da yawa suka gudu suka bar ladansu.
"Idan ka zagaya nan za ka ga wurare da yawa manoma 'yan uwa duk sun gudu. Man da za ka saya da tsada za ka saya. Ga kwari maganin feshi yana tsada. Duk kusan kwana uku sai ka saya. Kayan da za ka kai a saya kuma farashi ya fadi warwas. Saboda haka da wanne manomi zai ji?"
A yanzu da gwamnatin Tarayyar Najeriya ke shirin kara samar da madatsun ruwa dari biyu don fadada noman rani da wadata jama'a da ruwan, sama wa manoman mafuta ta cushewar kasuwa a duk shekara da ingantattun iraruwa da magungunan feshi masu rangwame za su taimaka wajen dorewar sana'ar da samun karfin guiwar yinta a ko ina.