1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro akan rikicin nukiliyar Iran

July 25, 2010

An ci gaba da ƙokarin samun mafita daga rikicin shirin nukliyar Iran

Shugaba Mahmoud AhmadinejadHoto: AP

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Iran,da Turkiyya da kuma Brazil, sun tattauna kan shawarwari da suka tsai da,na samar da mafita dangane da tankiyar da ake yi akan shirin nukliya na ƙasar Iran. A ganawar, wacce ita ce ta farko da ƙasashen guɗa ukku suke yi, tun bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ƙaƙaba wa ƙasar Iran takunkumi karya tattalin arziƙi a mataki na huɗu, ƙasashen Turkiyya da Brazil sun buƙaci ƙasar Iran ɗin, da ta ci gaba da tattaunawa cikin haske da ƙasashen yammacin duniya da ke zarginta da ƙera makaman Nukliya.

A cikin watan Mayun da ya gabata, Iran da ƙasahen Brazil da Turkiya, sun ba da shawara da a sarrafa sinadirin uranium ɗin ƙasar a wata ƙasa ta daban domin tantance gaskiyar lamarin.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas