Taro kan makomar kotun ICC
November 24, 2016Talla
A yayin da kasashen da suka hadu suka kafa kotun hukunta manyan laifukan kasa da kasa ta ICC da ke birnin Hague ke can suna wani taron nazarin makomar kotun, Najeriya ta ce ba ta da shiri fita a cikin kotun da ke kallon tawaye daga kasashe na nahiyar Afirka.