1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tsakanin EU da China a birnin Prage na Jamhuriya Chek

Sadissou YahouzaMay 20, 2009

Tawagogin China da na Ƙungiyar Tarayya Turai sun tattana a birnin Prage , a game da hanyoyin bunƙasa cinikayya tsakanin ɓangarorin biyu

Taron EU da China a birnin PrageHoto: picture-alliance/ dpa

A wannan larabar ce, tawagogin China da na Ƙungiyar Tarayya Turai suka shirya wani taro a birnin Prague na Jamhuriya Chek, inda suke tattana batutuwan da suka jiɓanci ma´amila tsakaninsu.

Mahalarta wannan taro a ɓangaren tawagar Ƙungiyar Tarayya Turai,sun haɗa da shugaban Jamhuriya Chek, Vaclav Klaus wanda ƙasarsa ke jagorancin EU da kuma shugaban hukumar zartaswa Jose Manuel Barosso, sai komishinan harakokin waje Havier Solana , sannan a ɓangaren China Firaminista Wen Jia Bao ke shugabancin tawagar.

Wannan haɗuwa dake matsayin ɗimke ɓarakar da ta kunno kai tsakanin China da EU, zata duba mahimman hanyoyin ƙara danƘon zumunci tsakanin ɓangarorin biyu, da bunƙasa cinikayya,mussamman a daidai wannan lokaci da kariyar tattalin arziki ta zama ruwan dare gama duniya.

Tun watan Disemba na shekara da ta gabata ,aka tsara gudanar da taron, amma daga bisani hukumomin China suka ɗage shi, a wani mataki na nuna rashin gamsuwa ga ganawar da aka yi tsakanin shugaban addinin Boudha Dalai Lama, da shugaban ƙasar France Nikolas Sarkosy ,bugu da ƙari shugaban Ƙungiyar Tarayya Turai a lokacin.

Saidai wannan akasi a ma´mila tsakanin China da EU, ba zai wani tasiri ba, ta fannin cinikayya ta la´akari da yadda ɓangarorin biyu ke sarƙe da juna ta fannin hada hadar cinikayya, inji Doris Fischer, wata massaniya a hukumar nazarin al´amuran siyasa da taimakon raya ƙasa a Jamus matakin da hukumomin China suka ɗauka ba abun mamaki ba ne:Wajibi ne ga Gwamnatin China ta ɗauki matakin da ta ɗauka na ɗage taron, don cika umarnin siyasarta ta cikin gida, to amma a zahiri al´amarin ba zai wata illa mai tasiri ba, ga ma´amilar diplomatiya.

Babu shakka a taron na yau, tawagogin China da na Tarayya Turai, za su yi masanyar ra´ayoyi cikin takatsantsan a game da rikiciny ankin Tibet, to saidai babban batun dake ajendar taron shine na hada hadar kasuwa.

Duk da matsalar tattalin arzikin da duniya ke fama da ita saye da sayarwa tsakanin China da ƙasashen EU na cikin halin gaba dai gaba dai.Ƙasashen EU ke matsayin na farko a ƙetare inda China ta fi saida hajojinta, to saidai a ɗaya hannun, bayan Amurika, China ke sahu na biyu, ta fannin hajojin da ƙasashenTarayya Turai ke saidawa a ƙetare.

A shekara da ta gabata, EU ta yi samu giɓin a ƙalla Euro miliyan dubu 170 a hada hadar kasuwancinta China.

A cewar Doris Fischer, taron na birnin Prage wata dama ce ta cimma hanyoyin magance matsalolin dake hana ruwa gudu a ma´milala tsakanin ɓangarorin biyu: Ƙungiyar TarayyaTurai na kokawa a game da yadda China ke rufe wasu ƙofofin kasuwaninta, abunda ya saɓawa dokokin Ƙungiyar cinikayya ta duniya, a yayin da China ke zargin EU da saka takunkumi ga wasu hajojinta.

A shekara da ta wuce hukumomin China sun ware zuzuruntu kuɗi Euro miliyan dubu ɗari biyar, ta fannin gine gine. ta wannan fanni ne watan Februaru da ya gabata, wata tawagar ƙasar China ta yi rangadi a ƙasashen Tarayya Turai, inda ta duba kamfanonin da masa´antun da suka cenceni samun kwangila.

Bayan gine ginen, ma´amilar cinikaya tsakanin Turai da China, na maida ƙarfi matuƙa a fuskar husa´ar ƙere-ƙere.

Mawallafi: Hein Matthias/Yahouza Sadissou Madobi

Edita: A.Tijani Lawal