1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen ƙungiyar haɗin kan larabawa

June 15, 2007

Yau ne ƙungiyar haɗin kann ƙasashen larabawa, ta fara zaman taro na mussamman a birnin Alƙahira na kasar Masar.

Mahimman batutuwa da ke ajendar wannan taro,sun haɗa da halin da ake ciki a Palestinu da kuma ƙasar Libanon.

Praministan Fouad Siniora na Libanon, ya gayyaci taron bayan kisssan gilar da a ka yiwa ɗan majalisar dokoki Walid Eido, ranar lataba da ta gabata.

Sannan ƙasashen larabawan za su mahaura a game da adawar ƙasar Syria, a kann batun kotun ƙasa da ƙasa da Majalisar Ɗinkin Dunia ta girka ,domin sharia´ar kisan tsofan Pamninstan Libanon Rafi Hariri.

Kazalika , taronzai duba, rikicin da ake cigaba da gwabzawa, tsakanin dakarun ƙasar Libanon, da yan takifen ƙungiyar Palestinawa ta Fath Al-Islam.

Hukumomin Libanon sun zargi Syria, da hannu a cikin wannan rikici , zargin da Damascus ta mussanta.

Masu kula al´ammura a yankin gabas ta tsakiya, sun hango cewar, taron na Alƙahira ba zai tsinana kamai ba, ta la´akari da mummuna rabuwar kanu, tsakanin ƙasashen larabawa, a game da batutuwan da tawagogin za su tantana akai.