1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen Duniya akan samar da zaman lafiya a Somaliya

May 22, 2010

Ƙasashen Duniya sun sake jaddada muhimmancin tallafa wa gwamnatin Somaliya

Hoto: AP

  Wakilai na gwamnatoci da shugabannin ƙasashen 55 na ƙasashen Afirka da yanki Asiya, da na Turai haɗe da mayan ƙungiyoyi na Duniya da ke yin taro a birnin Istambul ,sun jaddada aniyarsu ta kawo ɗauki ga hallartaciyar gwamnati riƙon kwarya ta ƙasar Somaliya

Da ya ke jawabi a wajan buɗe taron sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, ya ce babbar hanyar da za ta zama ma fi a-Ala wajan sake dawo da kwanciyar hankali a ƙasar ta Somaliya, ita ce ta taimakawa gwamnatin akan yunƙurinta na sake sasanta tsakanin al-umar ƙasar, tare da yin yaƙi da yan aware .

Gwamnatin dai ta ƙasar Somaliya wace ke da taƙaitacen iko da birnin  Mogadishio, na kan hanyar ƙara samu agajin ƙasashen duniya wajan sake kwato ƙasar daga hannu masu fafatikar kishin adinin islama  .

Mawallafi: Abdurahman Hassane Edita: Zainab Mohammed