1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen larabawa akan Siriya a Iraƙi

March 29, 2012

Wasu abubuwa masu nasaba da boma-bomai sun tarwatse a kusa da ofishin jakadancin Iran dake kusa da yankin nan da aka fi karfafa matakan tsaro mai suna Green zone a Bagadaza.

Kuwait's emir, Sheik Sabah Al Ahmad Al Sabah, center, attends the Arab League summit in Baghdad, Iraq, Thursday, March, 29, 2012. The annual Arab summit meeting opened in the Iraqi capital Baghdad on Thursday with only 10 of the leaders of the 22-member Arab League in attendance and amid a growing rift between Arab countries over how far they should go to end the one-year conflict in Syria. (Foto:Karim Kadim/AP/dapd)
Hoto: dapd

Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron shugabannin ƙasashen larabawa a fadar gwamnatin Irakin a wannan alhamis ɗin. Tuni dai hukumomin Irakin suka sanar da ɗaukar tsauraran matakan tsaro da suka hadar da tura jami'an tsaro dubu 100, zuwa sassa daban daban na birnin na Bagadaza. Daura da wannan an ɗauki matakan takaita zirga zirgan ababan hawa, da ma amfani da wayoyin tafi da gidanka na Salula. Ana saran shugabannin larabawan za su amince da daftarin da jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan ya gabatar dangane da warware rikicin siriya, tare da sanya shugaba Bashar al-Assad ya aiwatar da alkawarin daya ɗauka na amincewa da dukkan batutuwa da aka gabatar. Tuni dai mahukuntan na Siriya suka ce ba zasu bada kai bore ya hau ba, dangane da duk wani batu da za'a ƙirkiro a wannan taro na kasashen larabawan.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal