Taron ƙoli tsakanin Angeller Merkel da Jacques Chirac
June 6, 2006shugabar gwamnatin Jamus Angeler Merkell, da shugaban ƙasar France Jacques Chirac, a garin Rheinsberg, da ke arewancin birnin Berlin.
Mahimman batutuwan da tawagogin 2, ke tantanawa a kai, sun haɗa da mattakan samar da masallahar shinfiɗa A ɗazun nan ne, a ka fara taron yini ɗaya tsakanin daftarin tsarin mulki, na ƙungiyar gamayya turai, bayan da ƙasar France, ta yi watsi da shi,a shekara da ta gabata.
Sannan, za su masanyar ra´ayoyin a game da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, a sakamakon matakin da Amurika ta ɗauka, na shiga cikin tanttanawar.
A ɗaya hannun, Merkel da Chirak, za su cenza miyau, a dangane da Jamhuriya Demokradiyar Kongo, bayan da ƙungiyar EU,ta amince, ta tura dakaru a wannan ƙasa, domin sa iddo, ga zabbukan da za a gudanar, a ƙarshen wata mai kamawa.