1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙoli tsakanin Angeller Merkel da Vladmir Putine

October 10, 2006

A birnin Dresde, da ke gabacin Jamus, an shiga tantanawa, tsakanin shugaban ƙasar Rasha, Vladmir Poutine, da shugabar Gwamnatin Jamus, Angeler Merkel.

Tawagogin ƙasashen 2, za su tantana batutuwa daban-daban, da su ka haɗa da, yaƙi da ta´danci, hulɗoɗi tsakanin Russie, da Tarraya Turai, mussaman ta fannin makamashi.

Angeller Merkel, da Vladmir Poutine,, za su anfani da wannan dama, domin masanyar ra´yoyi, a game da batun rikicin makaman nuklear ƙasashen Iran, da Korea ta Arewa.

Sannan shugabar gwamnati Jamus, za taɓo batun yancin faɗin albarkacin bakin yan jarida, a Russie, ƙasar da ta yi ƙaurin suna, wajen ƙuntatawa yan Jarida.

Gobe idan Allah kai mu, shugaban ƙasar Russie, zai gana da shugabanin kampanoni da masana´antu, na Jmaus a birni Munich da ke kudancin ƙasar.

A sakamakon wannan taro, ana sa ran ɓangarorin 2, su rattaba hannu, a kan yarjeniyoyi daban-daban, ta fannin saye da sayarwa.