1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙolin ƙasashe G 20 a Mexico

Zainab MohammedJune 19, 2012

Ƙungiyoyi masu zaman kansu a tarayyara Jamus sun ce ko ɗaya basu tsammanin taron ƙasashe masu ci gaban masana'antun zai samar da mafita dangane da matsalolin yunwa da sauyin yanayi da Duniya ke fuskanta a halin yanzu

Leaders of the G20 nations gather for a group photo at the G20 summit in Los Cabos, Mexico, June 18, 2012. Pictured are (front row, L-R) U.S. President Barack Obama, China's President Hu Jintao, Mexico's President Felipe Calderon, South Korea's President Lee Myung-bak, South Africa's President Jacob Zuma, (second row, L-R) Australia's Prime Minister Julia Gillard, Germany's Chancellor Angela Merkel, India's Prime Minister Manmohan Singh, British Prime Minister David Cameron, Canada's Prime Minister Stephen Harper and Japan's Prime Minister Yoshihiko Noda. REUTERS/Jason Reed (MEXICO - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Silvia Holten, ta ce a ra'ayinta ƙasashen na G20 na da alhakin shawo kan matsalolin da ƙasashen duniya ke fama da shi. Mai magana da yawun ƙungiyar tallafawa ƙananan yara mai suna World Vision ta ce ta halarci taron da kwanoni uku. kwano ɗaya shinkafa ce a ciki, mai yawon hanun ƙaramin yaro guda domin nuna wa duniya yawan abincin da ƙananan yara kan ci su rayu. A na biyun kuma shima shinkafar ce amma cikin hannun magidanci wanda ke nuna cewa ko da an ƙara yawar shinkafar ba daƙile matsalar za'a yi ba:

Ta ce: "Suna buƙatar nama, hatsi, 'ya'yan itace da ganyayyaki domin su samu su gina jiki, idan ba haka ba, bayan shekaru biyu na haihuwa sai su shiga wani hali wanda da ƙyar ne a fid dasu kuma haka zasu cigaba da rayuwa kuma wannan na da illa ga tattalin arziƙin ƙasashen".

Jörn Kalinski daga ƙungiyar agaji ta Oxfam reshen Jamus ya ce yana tantamar ko batun samar da tsaro tra fuskan abinci zai sami wani cigaba a wannan taro na ƙasashe masu manyan masana'antu na G20. Kuma hakan duk da cewa shugaban ƙasar Mexico Felipe Calderon ya sanya shi kan gaba a taron, yana da nasa manufar domin mutane milliyan 52 ne ke zama cikin talauci a ƙasarsa wato kashi 46 cikin 100 na al'ummar ke nan.

Obama da MerkelHoto: Reuters

Ya ce "yanzu abunda muke ji daga taron shine, ba kan waɗannan abubuwan ake tattaunawa ba, batutuwa irin su abincin da ba'a shukawa da takin zamani, da illolin hauhawan farashin kayayyakin abinci da mutun bai san yadda zai yi da su ba."

Haka nan kuma Kalisnki na ganin cewa 'yan siyasan da suke taron na Los Cabos a ƙasar Mexico sun fi bada ƙarfi wajen tattauna rikicin euro, ta haka kuma duk wata magana ta tsaro a fanin abinci, da kuma tattaunawar harkokin da suka shafi ɗorewar ayyukan raya ƙasashe da ma hanyoyin samar da tallafin ayyukan muhalli duk sun koma baya, kuma a ra'ayinsa kamata yayi shugabar gwamnatin Jamus ta ƙara karfi ta kuma zuba jari a waɗannan abubuwa da ya lissafa:

Ya ce "ina da buƙatar ganin shugabar gwamnatin Jamus ta fayyace cewa kaso mafi yawa na daga kuɗaɗen harajin da ake warewa dan cigaban Turai, ana warewa kuma dan zuba jari kan ayyukan raya ƙasa da na kare muhalli a duk faɗin duniya."

Jose Manuel BarrosoHoto: Reuters

Wannan ra'ayi ya zo daidai da na Peter Wahl daga ƙungiya mai zaman kanta na WEED wacce ke da rajin kare tattalin arziƙin duniya da ci-gaban ƙasashe. Wanda ya bayyana cewa taron ƙolin na ƙasashe masu manyan masana'antu na G 20 musamman ma wajen ayyukan da zasu inganta tattalin arziƙi ta hanyar kyautata muhalli. Wahl kuma ya yi sukar cewam a'aikatan ƙungiyoyi masu zaman kansu a maimakon wakilan tattalin arziƙin ƙasashen da ke taro da manyan ƙasashen basu bada wakilcin da ya dace ba a Mexico.

Ya ce " muna so mu nemi da a tabbatar da cewa a taron da za'a gudanar nan gaba, za'a ga ƙungiyoyin fararen hula, kuma kasancewarsu a taron zai inganta irin matakan da ƙasashen na G 20 ke ɗauka.

Ƙungiyoyin dai sun gabatar da buƙatar ƙasashen su yi aiki tare da su kasancewar suna aiki kusa-kusa da ƙasashen da ke fama da waɗannan matsaloli.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar