1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar ƙasashen Larabawa game da Siriya

July 3, 2012

Rabuwar kanu tsakanin 'yan adawar Siriya ya kawo cikas ga ɗaukar matakai kan gwamnatin Bashar al-Assad

Syrian National Council (SNC) leader Abdel Basset Sayda listens to a journalist as he attends the Syrian opposition conference in Cairo July 2, 2012. Members of Syria's opposition and Arab and other foreign ministers begin a two-day conference in Cairo. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Kungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa tare da haɗin gwiwar gamayyar ƙasa da ƙasa, ta shirya zaman taro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, domin tattana rikicin ƙasar Siriya.

A jawabin da ya gabatar, Sakatare Janar na ƙungiyar ƙasashen Larabawa Nabil El Araby, ya yi kira da babbar murya ga 'yan adawar ƙasar Siriya su haɗa kai domin fuskantar dakarun shugaba Bashar Al-Assad.

An dai samun rabuwa kanu mai ƙarfi tsakanin ƙungiyoyi daban-daban masu adawa da gwamnatin Siriya, inda wasu daga cikinsu su ka ƙauracewa taron.

Itama Komishinar kare haƙƙoƙin bani Adama ta Majalisar ɗinkin Duniya Navi Pillay, ta zargin gwamnati da 'yan adawar Siriya da hallaka fara hulla.Daga farkon wannan rikici zuwa yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta mutane fiye da dubu 16 da suka rasa rayuka a cikin wannan rikici.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu