Wakilan Afirka da nahiyar Turai sun yadda da daukar matakan ilmantar da matasa da amfani da ci-gaban kirkirien fasaha, domin shawo kan kalubalen kaura daga Afirka zuwa Turai.
Yadda matasa ke tururuwar yin kaura daga Afirka zuwa nahiyar TuraiHoto: Hazem Ahmed/AP/picture alliance
Talla
Wakilai sama da 100 ne daga kasashen Afirka da nahiyar Turan suka hallara a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, a kokarin shawo kan matsalar ta kaurar da matasa ke yi daga nahiyar Afirka zuwa Turai ta haramtacciyar hanya. Taron da suka yi a karkashin kudurin Rabat da ya samar da dama ta aiki tare da nufin yi wa matsalar taron dangi, domin a zamanantar da ita. Kaso 30 na bakin da ke kaura daga Afirka zuwa Turan dai, dukkaninsu matasa ne da wadanda ke da kanana shekaru da ba su mallaki hankalinsu ba.
Tunawa da bakin haure a Lampedusa
Lampedusa waje ne da bakin haure da ke son zuwa Turai kan je. Mahamadou Ba dan Senegal ne da ke zaune a Portugal, kamar sauran bakin haure shi ma ya taba zama a Lampedusa. Hotonsa na nuna halin da bakin haure ke ciki.
Hoto: Mamadou Ba
Kofar Lampedusa
Tsibirin Lampedusa da ke kasar Italiya waje ne da bakin hauren da ke son shiga Turai kan je. Mahamadou Ba dan kasar Senegal na zaune a Portugal tun shekara ta 1997 kuma ya sha zuwa Lampedusa. Mutumin dan rajin kare hakkin bil adama ne kuma hotonsa a nan na nuna irin halin da bakin haure suka shiga a tsibirin Lampedusa da tekun da ke kusa da shi.
Hoto: Mamadou Ba
Jiragen ruwa sun zama tamkar wata makabarta
Jiragen ruwan nan da makamantansu sun zame wa bakin haure tamkar wata makabarta. Galibin bakin haure kan isa Lampedusa ne da irin wadannan kananan jiragen ruwa inda su kan gamu da hadarin da ke yin ajalinsu. Hadari mafi muni ya auku ne ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 2013 inda mutane 366 suka mutu yayin da sojin ruwan Italiya suka ceto mutane 200 a cikin watan Janairun da ya wuce.
Hoto: Mamadou Ba
Mutuwa kan hanyar neman rayuwa mai inganci
Ana daukar Lampedusa tamkar wata makabarta ga dubban bakin haure. "Mutane na mutuwa don neman rayuwa mai inganci" kamar yadda Mamadou Ba ya nunar. Kimanin mutane 400 ne suka rasu a watan Oktober shekarar 2013 lokacin da wasu jiragen ruwa biyu suka yi hatsari yayin da suke kan hanya daga arewacin Afirka zuwa Lampedusa. Galibin wanda suka rasu sun fito ne daga kasashen Eritrea da Somaliya.
Hoto: Mamadou Ba
Abubuwan da za a tuna bakin haure da su
Galibi ba a da cikakkun bayanai game da asalin bakin hauren da kan rasu a Lampedusa lokacin da suke kokarin shiga nahiyar Turai. Yawanci ababen da ake tunawa da mutanen su ne irin wadannan rigunan da sauran kayayyakin da ake samu a jikin jiragen ruwan da suka nutse da bakin hauren da ke cikinsu.
Hoto: Mamadou Ba
Gidan adana kayan bakin hauren da suka rasu
Akwai wani gida na adana kayan tarihi musamman na bakin hauren da suka rasu sakamakon nutsewar jiragen ruwansu. Kayan sun hada da fasfuna da hotuna da kuma wasiku. Mamadou Ba ya ce kayan na sawa a tuna da wadanda suka rasu. Har wa yau kayan kan sa a fahimci yadda bakin haure suke da irin mafarkin da suke da shi.
Hoto: Mamadou Ba
Abubuwan da bakin haure kan yi yau da kullum a kan teku
Bakin haure kan gudanar da irin dabi'un da suka saba kan teku lokacin da suke kokarin ketarowa zuwa nahiyar Turai. Galibi irin wannan yunkuri nasu na kasancewa mai hadarin gaske. Babu dai tabbas ko irin wadannan tukwanen da ke ajiye a gidan adana kayan tarihin bakin hauren na wadanda suka mutu ne ko kuma wanda suka rayu amma kuma kayansu suka salwanta.
Hoto: Mamadou Ba
Tunawa da rayukan wadanda suka rasu
Akwai wurare da dama da ke tuna wa mutum bakin hauren da ke zaune a tsibirin Lampedusa mai tsawon mil tara. "Wajen kan sa a tuna da wanda ke raye da kuma wadanda suka rasu'' kamar yadda Mamadou Ba ya nunar. Lampedusa dai na da nisan kilomita 205 kudu da tsibirin Sicily na Italiya kazalika yana makotaka da Tunisiya wadda tazararsu ba ta wuce kilomita 130 ba. Lampedusa wani tsani ne na shiga Turai.
Hoto: Mamadou Ba
Bukatar fidda sabbin manufofi kan bakin haure a Turai
Wannan wajen da ke zaman maboya lokacin yakin duniya na biyu wata alama ce ta hadewar kungiyar tarayyar Turai. A cikin watan Fabrairun da ya gabata wakilan kungiyoyin fararen hula 400 sun yi zanga-zanga inda suka fidda sanarwa kan bukatarsu ta neman sabbin manufofi kan bakin haure a Turai. Kungiyoyin sun bukaci karin mutunta 'yancin bakin haure duba da yadda da dama ke mutuwa a kan iyakokin Turai.
Hoto: Mamadou Ba
Lampedusa daura da kogin Bahar Rum
Mazauna wannan karamin tsibiri na Lampedusa da ke kogin Bahar Rum kusa da Sicily da arewacin Afrika na fatan samun ingantacciyar rayuwa. Da dama dai na ganin idan aka yi gyare-gyare kan manufofin kasashen Turai game da bakin haure, kwararar bakin da ake samu da kuma hadurran da suke gamuwa da su za su ragu matuka.
Hoto: Mamadou Ba
Hotuna 91 | 9
Daukacin kasashen Turai dai na aiki ne da hadin guiwar kasashen Afirka da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, domin dakile matasan da ke kauran wadanda kaso 20 cikin 100 ke bin hanyoyi da suka sabawa doka. Jamhuriyar Nijar dai ta zama wata hanya da masu kaura ta hanyar da ba ta dace ba daga yankin Afirka ta Yamma ke bi, domin zuwa nahiyar Turai. Najeriya dai na cikin kasashen da wannan matsala take da girman gaske, inda gwamnati ta bayyana daukar matakai na shawo kanta. Nahiyar Turai da Afirka na son ganin yadda za su zamanantar da tsarin kaurar da matasa ke yi ta hanyara koya masu ilimi da sana'oi, domin su iya kaura tare da ilimi da sana'a mai tsari da mutunci da kuma kima.