Ƙasashe da Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na zaman taro a Munich a game da tsaro
February 7, 2009
Nan gaba a yau ne a birnin Munich na nan ƙasar Jamus ake kammalla zaman taro karo na 45, a game da batun tsaro da kwanciyar hankali a duniya.
Tawagogi ɗari ukku daga ƙasashe dabam daban na duniya, ke halaratar wannan muhimmin taro, wanda suka haɗa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy, da kuma mataimakin shugaban ƙasar Amurika Joe Biden.
A ranekun juma´a da asabar suntafka mahaurori a game da hanyoyin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma ƙara cuɗe ni in cuɗe ka tsakanin ƙasashen duniya.
A jawabin da ya gabatar ministan harakokin wajen Jamus Frank Walter -Steinmeier, ya danganta taron na Munich a matsayin wata dama ta shinfiɗa zaman lafiya mai ɗorewa a duniya, ya kuma yaba saban matakin da shugaban ƙasar Amurika Barack Obama ya ɓullo da shi a game da warware rikicin nukleya da ƙasar Iran.
" Ina kyautata zaton yanzu za a samu cenjin al´ammura a fadar mulkin Washington.
Bayan shekaru da dama na ƙiƙi-ƙaƙa, sabuwar gwamnatin Amurika ta bayyana aniyarta, ta tattanawa ƙeƙe da ƙeƙe da hukumomin Tehernan,Wanan babban cigaba ne, saidai ina kira ga Iran ta bada haɗin kai."
A nasa jawabi mataimakin shugaban ƙasar Amurika, Joe Biden,yayi amfani da wannan dama inda ya bayyana sabuwar siyasar gwamnatin Amurika ta fannin tsaro.
Sannan yayi tsokaci a game da rikicin nukleyar Iran:
" za mu tattanawar gwa da gwa da hukumomin Iran, mun faɗawa juna gaskiya, kuma mu basu zaɓi, au su ci gaba da nuna taurin kai su zama saniyar ware a fagen siyasar duniya, au kuma su bada haɗin kai a dinga damuwa da su."
Saidai shugaban Majalisar Dokokin Iran wanda kuma ya lakancvi kabli da ba´adin rikicin nuklear ƙasar wato Ali Larijani, ya maida martani da kakkausar harshe tare da cewa:
" Shin kuna tunanin barazana da hurjin mussa da parfaganda ta kafofin sadarwa zasu sa Iran ta cenza aƙida ? ko kussa, ya kamata wancen bangare shima wato Amurika ya gane kura kuransa kuma ya gyare ta hanyar cenza sallo"
Shi kuwa Shugaban Ƙungiyar tsaro ta NATO, Jaap de Hoop Scheffer,a jawabinsa ya zargi aniyar ƙasar Russia, ta girke cibiyoyin yaƙi a yankunan Georgiya Abkhaziya da Ostesiya ta kudu.
Wannan mataki a cewar NATO ya saɓawa siyasar duniya ta samar da zaman lafiya.