Taron bitar kayan tarihi a Kano
June 26, 2009Talla
Hukumomin kula da tarihi da al´adu na ƙasashen Afirka Ta Yamma sun shirya wani taron bita a Kano a kwanakin baya don a zaɓo muhimman wuraren tarihi waɗanda za su kasance ƙarƙashin kulawar hukumar raya al´adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO.
Ƙasashen Afirka Ta Yamma dai su ne waɗanda ba su sami cikakken gata na kulawar kayayyakin tarihinsu a ƙarƙashin wannan hukuma ba musamman idan aka yi la´akari da ƙasashen Afirka Ta Arewa, waɗanda wasu daga cikinsu sun mallaki kayayyakin tarihi na dubban shekaru.
An nuna kyakkyawan fatan cewa wannan yunƙuri na UNESCO zai sa a ceto kayan tarihi na wasu ƙasashe da suke neman ɓacewa daga doron ƙasa baki ɗaya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Madobi