Taron bitar ta'addanci a Spain
March 8, 2005A daidai ranar ta 11 ga watan maris na shekarar da ta wuce, wasu musulmi masu zazzafan ra’ayi suka kai hare-hare akan wasu jiragen kasa guda hudu da suka saba jigilar ma’aikata da sanyin safiya. Mutane 191 ne suka yi asarar vrayukansu sakamakon wannan danyyen aiki. A binciken da mahukunta suka gudanar dai an tabbatar cewar masu zazzafan ra’ayin su kai wadannan hare-hare ne domin ramuwa akan hannu da kasar Spain ke da shi wajen yakar kasar Iraki. Wannan matakin ya taimaka jam’iyyar Socialist mai adawa da yakin kasar Irakin ta cimma nasarar zaben da ya biyo bayan wannan harin da kwana uku. Bayan wannan zabe, sabon P/M da aka nada Jose Luis Zapatero ya bayyana cewar babbar manufarsa ita ce yakar dukkan nau’i na ta’addanci daga tushensa. Kuma ita ainifin wannan manufar ce za a mayar da hankali kanta a taron kolin da ake farawa yau talata a birnin Madrid a karkashin taken, Demokradiyya, Ta’addanci da tsaro. Sai dai kuma ba gwamnatin Spain ce ta kira wannan taro ba, wata kungiya ce da ake kira Club of Madrid da ta kunshi tsaffin shuagabannin kasashe kamarsu Clinton na Amurka ko Gorbatchov na tsofuwar tarayyar Soviet, wacce kuma a yanzun take karkashin jagorancin tsofon shugaban kasar Braszil Fernanondo Henrique Cardoso. Kwararrun masana kimanin 250 zasu yi tsawon yini biyu suna musayar ra’ayi domin kuwa maganar ta’addancin ta shiga wani sabon babi tun bayan 11 ga watan maris na shekarar da ta wuce a cewar Jesus Nunez, kwararren masani akan al’amuran ta’addanci daga kasar spain, wanda kuma ya ci gaba da cewar:
Tun bayan abin da ya faru a ranar 11 ga watan maris na bara jami’an ‚yan sanda da hukumar leken asiri ke bin diddigin duk wani abin da ka iya zama barazana ga tsaron lafiyar jama’a fiye da yadda lamarin ya kasance a zamanin baya.
Ita dai kasar spain, wacce a zamanin baya ta sha fama da ta’addancin kungiyar aware ta ETA, a yanzu tana fuskantar barazanar zama wani dandali na ta’addanci ga wasu musulmi masu zazzafan ra’ayi. Ana dai fata taron na kasa da kasa zai ba da nagartattun shawarwari akan matakan da suka cancanta wajen tinkarar matsalar ta ta’addanci, kamar yadda aka ji daga P/M Jose Luis Zapatero. An dai saurara daga bakinsa yana mai cewar:
Shawarar da zan ba wa ‚yan siyasa da ‚yan socialist da kuma masu sha’awar mulkin demokradiyya tsantsa shi ne a gabatar da wata yarjejeniya ta kasa da kasa domin yaki da ta’addanci. Irin wannan yarjejeniya tana iya zama abin koyi ga kafofi na kasa da kasa kamar dai MDD. Kasar Spain a shirye take ta dauki matakin farko bisa manufa.
Ana sa ran halarcin shuagabannin kasashe da dama a ranar karshe ga taron kolin, ko da yake babu wani cikakken bayani a game da ko shin shugaban Amurka Goerge W. Bush zai halarcin zauren taron ko sakatariyarsa ta harkokin waje. Kazalika shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da shugaban Faransa Jacques Chirac. Amma ministan harkokin waje Joschka Fischer zai halarci zaman juyayin da za a yi a ranar 11 ga wata.