1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar BRICS ba tare da Xi Jinping da putin ba

July 6, 2025

Shugabannin kasashen kungiyar BRICS da tattalin arzikinsu ke habaka duniya na ganawa a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.

Taron BRICS na Brazil
Taron BRICS na BrazilHoto: Ricardo Stuckert/PR

Shugabannin kasashen kungiyar BRICS da tattalin arzikinsu ke habaka duniya na ganawa a birnin Rio de Janeiro na Brazil a yau Lahadi a taronsu na koli na kwanaki biyu.

Kasashen na BRICS sun hada da Brazil da Rasha da Indiya da China  da Afirka ta Kudu, kuma a farkon shekarar da ta gabata, kasashe kamar Iran da Habasha da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa  suka shiga cikin kungiyar, yayin da Indonesiya ta shiga cikin watan Janairun bana.

Taron kolin, wanda Brazil ke jagoranta, na shirin tattauna manufofin lafiya da fasahar kirkirarriyar basira wato AI, da ma sauyin yanayi.

Sai dai a karo na farko, shugaban kasar China, Xi Jinping, ba zai halarci taron a zahiri ba, inda zai aika wakili.

Haka shi ma, shugaban Rasha, Vladimir Putin ba zai halarci taron ba saboda kotun duniya ICC ta fitar da umarnin kama shi saboda mamayar da Rasha ta kai Ukraine tun 2022.