1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ko zaá cimma burin rage barazanar ɗumamar yanayi ?

December 6, 2009

kyakyawar fata ga taron duniya kan sauyin muhalli.

Taron manyan shugabanin duniya.Hoto: picture-alliance/ dpa

Akwai kyakkyawar fata ga taron ƙasashen duniya bisa kare mahalli na Majalisar Dinkin Duniya a Kopenhagen. Wala Allah ko a samu biyan buƙata koma akasin hakan. Ko za'a samun cimma burin ƙayyade barazanar ɗumamar yanayi kamar yadda aka tsara taron, waɗannan sune ayoyin tambaya da ake neman samun amsarsu a taron.

Yvo der Boer Sakataren hukumar kula da mahalli ta Majalisar Dinkin Duniya na mai raáyin cewa taron na Kopenhagen zai kawo sauyi mai inganci dama samar da kuɗi, amma wani batu daban za'a samu, idan dai babu taron na Kopenhagen.

Ga mutane irin su Yvo der Boer, babu abin tambaya bisa yunƙrin ƙasashen duniya na yaƙi da sauyin yanayi, a'a sai dai a tambayi wane irin matakin gaggawa suka yi don cimma burin. A gaskiya hukumar kare malli ta Majalisar Dinkin Duniya tana ganin ɗaukar matakin taƙaita ɗumamar yanayi wani abu ne da ya zama tilas. Ƙasashen duniya su cimma yarjejeniyar kawar da barazanar da iskar gas ke yiwa mahalli, dama wassu ababen rayuwa na yau da kullum. "Ɗumamar yanayi wani babban mahimmin ɓangare ne, amma muna maganar yadda tsadar makashin da muke anmfani da shi ya ƙaru, samar da makamashi daga tsaftatacciyar iska. Da irin kimiyar da muke anfani da ita, waɗanda a yanzu ita ma ta tsufa"

Yvo de Boer Sakataren hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/ dpa

Don haka ne mutane irin su Peter Thimme na ƙungiyar zuba jari da cigaban tattalin arziki na ƙasar Jamus yake cewa akwai mahimman ɓangarorin da ya kamata sufi maida hankali.

"Ko nawane yawan guɓatacciyar iskar gas anan gaba za'a samu, ko nawane yawan ta wanda za'a rage, ta yaya za'a samar da kuɗin yin hakan, da waɗanne kayan zamani zamuyi aiki dasu wajen cimma buri"

Shima kansa shugaban hukumar kare mahalli ta Majalisar Dinkin Duniya Achim Steiner ya amince da cewa bawai fasahar ce basu da ita ba, amma dai ƙasashen duniya ne kawai basu da hadin kai. "Muna da fasahar muna da kimiya, muna da kafar tattalin arzikin, abinda muka rasa a yanzu shine ƙarfin ƙudiri na ƙasashen duniya wajen cimma burin da muka sa a gaba"

Tururin hayakin masanaántuHoto: AP

Yanzu fatan ƙasashen duniya shine yadda manyan masu ƙarfin masana'atu ke bunƙasa masana'antun nasu da kuma buƙatar ware maƙudan kuɗaɗe don yaƙi da ɗumamar duniya.

Mawallafa : Jeppesen Helle /Usman Shehu Usman

Edita : Abdullahi Tanko Bala