1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Taron Dattawan Arewa kan tsaro

November 21, 2024

Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewa (ACF) a Najeriya da wata kungiyar Arewa da ke fafatukar dabbaka mulkin dimukuradiyya sun kammala wani taro kan hadin kan Arewa da magance matsalar tsaro.

Nigeria Tinubu Gouverneur Treffen
Hoto: Ubale Musa/DW

Mahalalta taron sun kuma tattauna hanyoyin rage fatara da talauci, tare da batun 'yan gudun hijira da samar da kyakkyawan yanayi da zai inganta zamantakewar al'ummar yankin. Sanata Ibrahim Ida shi ne mukaddashin shugaban kungiyar ta Dattawan Arewa ACF, ya kuma bayyana cewa sun tattaru ne da nufin kara kulla dankon zumunci da kuma yin nazari kan muhimmancin da ke tattare da hada kan al'ummar yankin arewacin Najeriya da kuma lalubu mafuta kan manyan kalubalen da suke janyowa Arewa koma-baya a bangaren samar da zaman lafiya da sauran abubuwan da ke hana ruwa gudu a yankin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani