Taron duniya akan sake gina Somaliya
May 7, 2013Kungiyar tarayyar Turai, ta bayyana kudirin bayar da kudi Euro miliyan 44 kwatankwacin dalar Amirka miliyan 58 a matsayin agaji ga kasar Somaliya. Kwamishinan kula da harkokin raya kasashe a kungiyar tarayyar Turai Andris Piebalgs, shi ne ya bayyana wannan kudirin a wajen babban taron duniya akan zakulo hanyoyin sake gina kasar Somaliya, wanda ke ci gaba da gudana a birnin London na Birtaniya. Ya ce babban abinda ya kamata a fi mayar da hankali akai shi ne sha'anin tsaro, wanda ya ce ba za a taba samun ci gaba mai ma'ana ba - in ba tare da shi ba.
Tun daga shekara ta 2008 dai, kungiyar tarayyar Turai ta bayar da agajin daya kai na kudi Euro miliyan dubu daya da miliyan 200 ga kasar Somaliya. Galibin kudin kuma sun sanya shi ne a sha'anin farfado da shari'a da samar da kayan aiki da kuma bayar da horo ga jami'an 'yan sanda.
Mawallafi : Yusuf Bala
Edita : Umaru Aliyu