1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai ta sauya taro zuwa ta bidiyo

Zainab Mohammed Abubakar
March 21, 2021

Taron kolin shugannin Turai da aka shirya gudanarw a birnin Brussels din kasar Beljium, ya koma ta bidiyo saboda ta'azzarar zagaye na uku na COVID 19 tsakanin kasashen nahiyar.

Coronavirus EU Videokonferenz Macron
Hoto: Getty Images/AFP/I. Langsdon

Shugaban majalisar Turai Charles Michel da ke shirya taron shugabannin, ya zartar da hakan saboda karuwar yaduwar corona, a cewar kakinsa Barend Leyts.

Taron dai zai tabo muhimman batutuwa da suka hadar da lalacewar dangantaka tsakanin Turai da Rasha da kuma Turkiyya, da kuma rashin kyakkyawan tsarin allurar rigakafin corona a bangaren membobin kungiyar ta EU.