Taron fayyace makomar Kosovo tsakanin Sabiya da Albaniya
July 25, 2006Talla
A karon farko tun bayan hare haren da jiragen saman yakin kungiyar tsaro ta NATO suka kaiwa birnin Belgrade a shekarar 1999, an fara shawarwari tsakanin shugabannin Sabiya da Albaniya game da makomar yankin Kosovo. Taron wanda ke gudana a birnin Vienna, yana samun halarcin shugaban Sabiya Boris Tadic da FM Vojislav Kostunica. A bangaren Albaniya kuwa shugaba Fatmir Seydiu da FM Agim Ceku ke wakiltar kasar. A hira da tashar DW ta yi da shi game da taron wanda wakilin MDD na musamman Martti Ahtisaari ke jagoranta, shugaban Albaniya Fatmir Seydiu cewa yayi.
Insert O-Ton Seydiu.