1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron G20: AU na dakon goron gayyata

September 6, 2023

Kungiyar Tarayyar Afrika ta ce har kawo yanzu ba ta samu goron gayyata a hukumance ba, domin halartar taron kasashe masu karfin masana'antu na G20 wanda za a gudanar a Indiya.

G20 Umweltminister in Indien
Hoto: Ajit Solanki/AP Photo/picture alliance

A makonnin baya firaministan Indiya Narendra Modi ya mika wa kungiyar AU tayin zama mamba na din-din-din a kungiyar ta G20 wacce ke samar da kashi 85 cikin dari na arzikin duniya. 

Karin bayani: Taron G20 ya karkata ga kasuwanci da tsaro

To sai dai a wata hira da manema labarai, mai magana da yawun kungiyar Ebba Kalondo ta ce yayin da ya rage kwanaki uku kacal a buda taron na birnin New Delhi har kawo yanzu AU ba sami goron gayyata a hukumance ba.

Karin bayani: An kasa cimma matsaya a taron G20

Kugiyar tarayyar Afrika dai mai ofishi a birnin Adis Ababa na kasar Habasha ta kunshi kasashe 55 wadanda ke samar da albarkatu da kudinsu ya haura biliyan 3.000 na dalar Amurka. Wannan ne ma ya sa a can baya shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana fatan sama wa Tarayyar Afrika gurbi a kungiyar ta G20 yana mai cewa abu ne da zai iya kara masu karfi.