Taron G7: Babu matsaya kan sauyin yanayi
May 27, 2017A cikin sanarwar bayan taron kolin yini biyu da suka kammala ranar Asabar da yamma a garin Taormina na gabar tekun kasar Italiya, shugabannin kasashen kungiyar G7 sun amsa cewa sun gaza magance bambamce-bambamce tsakaninsu a kan sauyin yanayi, bisa turjiya daga kasar Amirka.
Sai dai sauran kasashe shida na kungiyar ta G7 sun amince kan alkawarin da suka dauka na aiwatar da yarjejeniyar Paris ta 2015 da ke da burin rage fidda hayaki da ke dumama doron kasa.
Shugaban Amirka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a mako mai zuwa Amirka za ta yanke shawara kan wannan batu.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela ta nuna rashin gamsuwarta da tattaunawar da G7 din ta yi kan sauyin yanayin.
Ta ce: "Tattaunawar da muka yi kan yanayin ta yi zafi amma ba ta gamsar ba. Shida daga cikinmu ko kuma in ce bakwai in an hada da kungiyar EU, mun fuskanci turjiya daga kasa guda daya. Abin nufi Amirka ba ta nuna alamun ko za ta zauna cikin yarjejeniyar Paris ba ko a'a. Ba mu yi wata-wata ba mun fito karara cewa mu shida daga kungiyar G7 hadi da EU za mu ci gaba mutunta yarjejeniyar."
Tattaunawa kan sauyin yanayi bata gamsar ba
Sanarwar cewa ta yi Amirka na yin bita kan manufofinta na sauyin yanayi da kuma yarjejeniyar Paris saboda haka ba za ta shiga cikin jerin kasashen da tuni suka amince da yarjejeniya ba. A kan haka Firaministan Italiya da ya karbi bakoncin taron kolin, Paolo Gentiloni ya ce sauran kasashen shida ba za su canja matsayinsu kan sauyin yanayi ba.
Ya ce: "Kamar yadda kuka gani a cikin sanarwa bayan taron kolin G7 a Taormina, an tattauna tsakani da Allah kan muhimman batutuwa in banda batun sauyin yanayi. Saboda haka ba za mu canja matsayinmu ko na miskala zarrati a kan sauyin yanayi ba, duk da cewa har yanzu Amirka ba ta yanke shawara ba. Ina fata za su dauki matakin da ya dace."
Matsaya kan wasu batutuwa
Shugabannin na G7 sun samu jituwa a kan batun ciniki da suka dade suna takaddama kai. Sun kuduri aniyar yaki da manufar kare masana'antun cikin gida da amfani da haraji na cikin gida da wasu ka'aidoji da ke fifita masana'antun cikin gida a kan takwarorinsu na ketare.
Shugabannin na G7 sun kuma gana da shugabannin Afirka biyar da aka gayyata a taron. Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya yi kira ga G7 da ta gaggauta daukar matakan kawo karshen rikicin kasar Libiya inda dubban bakin hauren Afirka ke bi don shiga Turai. Shugaban ya kuma soki G7 da rashin cika alkawuran da ta dauka na yaki da talauci a yankunan da suka fi fama da talauci a yammacin Afirka.