Taron G7 kan kasuwanci ya gaza samun matsaya
June 3, 2018Talla
Taron dai ya watse ne baram-baram ba tare da mahalarta sun iya fitar da wata sanarwar hadin gwiwa ta karshen zaman taro ba, inda duk bangarorin kowa ya gudanar da nashi taron manema labarai domin bayyana matsayinsa.
Daga daya bangaren dai ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashen na Turai dai sun bayyana rashin amincewa da tsarin kasuwancin kasar ta Amirka inda suka yi kira ga Shugaba Donald Trump da ya yi watsi da matakinsa na dora haraji kan bakin karfe da kuma karfen sanholo
Sai dai bangarorin biyu sun yi alkawarin sake haduwa a mako mai zuwa a birnin Quebec na Kanada domin sake tattauna wannan rikici na kasuwanci da ke kara kamari tsakanin kasashen na Turai da abokiyar huldar kasuwancinsu ta Amirka.