G7. Sakon samar da zaman lafiya a duniya
May 19, 2023![Themenpaket - G7 Summit Hiroshima Japan](https://static.dw.com/image/65675626_800.webp)
Talla
A farkon taron kolinsu a Hiroshima, sun gudanar da bikin ajiye furanni na tunawa da wadanda harin bam din nukiliya na farko ya rutsa da su a yaƙin duniya na biyu. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewa, tarihin birnin ya zama abin tunawa da alhakin da ya rataya a wuyan zaman lafiya da tsaro a duniya. An yi raga-raga da birnin na Hiroshima gaba daya a harin nukiliyar Amurka a watan Agustan shekara ta 1945, kafin harin bam na biyu na Atom bam da aka harba a Nagasaki inda mutanne mutane sama dubu dari suka mutu.
.