1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron gaggawa kan Fari a yankin kusurwar Afrika a birnin Rome

July 25, 2011

Yankin kudancin Somaliya na ci gaba da kasancewa inda yunwa ta fi yin ɓarna sakamakon Fari

Jacques DioufHoto: AP

Shugaban hukumar kula da Noma da samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya bayyana bukatar ɗaukar matakan gaggawa wajen fuskantar bala'in fari da yunwa da ƙasashen yankin kusurwar Afrika ke fuskanta. Jacques Diouf ya yi wannan furucin ne a wajen taron gaggawa dangane da wannan matsalar a birnin Rome. Ministan harkokin noma na Faransa Bruno Le Maire da ke halartan taron na Rome, yace ƙasashen Duniya sun yi sakaci wajen samar da da ingantaccen abinci damin kare in wannan yanayi a Duniya. Taron na birnin Rome ya zo ne a daidai lokacin da yankin kusurwar Afrikan ke fuskantar mafi munin yunwa da karancin abinci a karon farko cikin shekaru 60 da suka gabata, wanda ya jefa mutane milliyan 12 cikin bala'in yunwa. A yau ne dai Bankin Duniya yayi alkawarin bayar da tallafin kusan Euro miliyan 350, domin aiwatar da harkokin Noma da za su tallafawa yankin da ke fuskantar fari a yankin kusuwar Afrika.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Halima Abbas