1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron gangami na ƙasashen Turai akan Libiya

March 11, 2011

Ƙasashen Turai sun kawo ƙarshen taronsu na gangami da suka gudanar a Brussels ba tare da cimma wata matsaya ba a game da yadda zasu tinkari rikicin Libiya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na musayar yawu da Sarkozy na Faransa a taron ƙolin EU akan LibiyaHoto: dapd

Sai dai shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun yi kira ga shugaban Libiya Muammar Gaddafi da yayi murabus ba da wata-wata ba. Kazalika shuagabannin sun yi Allah Waddai da hare-haren da ake kaiwa kan farar hula a Libiya.

A yayinda shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ke nuni da cewar Faransa da Birtaniya a shirye suke su yi katsalandan idan zarafi ya kama, a nata ɓangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel gargaɗi tayi da taka tsantsan ka da a ɗauki wani mataki a cikin garaje.Ko da yake tayi kira ga Gaddafi da ya janye daga kujerar mulki. An saurara daga bakin shugabar gwamnatin ta Jamus tana mai faɗi cewar:

"Duk wani dake yaƙar al'umarsa ba abokin hulɗar ƙungiyar tarayyar Turai ba ne. A saboda haka muke kira ga Gaddafi da yayi murabus ba da wata-wata ba kuma zamu yi iyakacin ƙoƙarinmu domin cimma matsaya ɗaya akan matakan takukumin da zamu ɗauka da tabbatar da cewar ba muyi hulɗa da Gaddafi nan gaba ba."

Sarkozy na kiran ɗaukar matakan soja akan Libiya


Sarkozy na goyan bayan matakan soja akan LibiyaHoto: AP

To sai dai kuma a yayinda shugabar gwamnatin ta Jamus ke batu game da matakan takunkumi wasu shuagabannin batu suke game da katsalandan soja, kamar dai shugaba Sarkozy na ƙasar Faransa, bayan tattaunawarsa da piraministan Birtaniya David Kamerun. An saurara daga bakin shugaban Faransar yana mai yin nuni da cewar ana iya ɗaukar matakan kariya idan har Gaddafi ya fara amfani da makaman guba ko kuma kai hari akan farar hula:

"Idan har Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito fili ta amince ita kuma ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa ta yarda sannan su kuma mahukuntan Libiyan da muka yi amanna da su suka buƙaci hakan, to Faransa da Birtaniya su ɗauki matakan kariya. Amma hakan zata kasance ne kawai idan Gaddafi ya fara amfani da makaman guba ko lugudan wuta ta sama akan farar hula, waɗanda ke zanga-zangar lumana."

Shi kuwa piraministan Birtaniya David Cameron cewa yayi wajibi ne ƙungiyar tarayyar Turai ta kasance a cikin shirin ko-ta-kwana domin fatattakar Gaddafi daga karagar mulki. Piraministan Birtaniyar ya ci gaba da cewar:

Shi ma piraministan Birtaniya David Cameron na ba da goyan baya ga matakan soja akan LibiyaHoto: dapd

"Lokaci yayi da Turai zata fahimci cewar ire-iren abin dake faruwa a arewacin Afirka wata sabuwar wayewa ce ta demokraɗiyya. Kuma kamata yayi mu ba wa waɗannan ƙasashe ƙwarin guiwa su bi hanya madaidaiciya ta demokraɗiyya. Lokaci yayi da Turai zata faɗa a fili cewar mun caɓa kurakurai a baya, amma a yanzu muna mika hannu ga ƙasashen domin yi musu tayin hulɗar zumunta da buɗe musu ƙofofin kasuwanninmu tare da madalla da fafutukar da suke yi domin tabbatar da 'yanci da demokraɗiyya a ƙasashensu."

To sai dai kuma duk da waɗannan bayanan duka-duka abin da shuagabannin ƙasashen ƙungiyar ta tarayyar Turai suka faɗa a cikin sanarwarsu ta bayan taro shi ne nem,an Gaddafi da yayi murabus ba da wata-wata ba. Sai kuma daidaituwar da suka cimma na ƙara tsawwala takunkumin tattalin arziƙi kan Libiya, inda ministan harkokin wajen ƙasar Hungary Jonas Martonyi ya nuna yiwuwar ɗora hannu akan ajiyar kamfanonin Libiya.

A kuma halin da ake ciki yanzu ana ci gaba da samun rahotanni masu jirkitaswa dangane da fafatawar da ake yi akan yankin Ras Lanuf mai arzƙin man fetur dake hannun 'yan tawayen a yayinda aka ce kimanin mutane dubu goma suka shiga zanga-zangar neman kakkaɓe Gaddafi daga karagar mulki a birnin Bengazi bayan sallar juma'a.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi