Taron gangami na jam'iyyu masu kyamar baki
January 29, 2016Jam'iyyun siyasa masu kyamar baki da adawa da Kungiyar Tarayyar Turai na kasashen Turai da dama sun gudanar da wani taron gangami a jiya Alhamis da a wannan Jumma'a a birnin Milan na kasar Italiya domin jaddada matsayinsu na kyamar Kungiyar Tarayyar Turai wacce ake bayyana da kasancewa ummulhaba'isan duk matsalolin da al'ummar kasashen Turai suke fiskanta a yau. Jam'iyyun masu kyamar bakin sun bayyana fatan samun hadin kansu wajen ruguza Kungiyar Tarayyar Turai dama maido wa kasashen Turai cikakken 'yancinsu. Marine Le Pen ita ce shugabar jam'iyyar Front National ta masu ra'ayin kyamar baki ta kasar Faransa
Ta ce "abin da ake bayyanawa a matsayin matsalar 'yan gudun hijira, ta bayyana karara illar da ke tattare da yarjejeniyar Schengen, kuma abin da ke wakana a yanzu zai taimaka ga ganin bayanta"
Wadannan jam'iyyun masu kyamar baki a kasashen Turai sun kuma jaddada burinsu na karbe milki a cikin kasashen Turai a 'yan shekaru masu zuwa wanda hakan zai ba su damar daukar matakin rufe iyakokin kasashensu da nufin gudanar da bincike dan fiskantar abin da suka kira barazanar masu kishin islama da ke adabar kasashen nahiyar.