Masar: Taron tantance bugun Al-Kur'ani
September 28, 2021Wannan zama dai zai bayar da dammar ci gaba da buga Al-Kur'anai da babu kura-kurai da yadasu a duniya. Kwamitin gyaran bugun rubutun Al-Kur'anin na kasar Masar kan yi zamansa a duk lokacin da bukata ta taso, domin bai wa madabbabo'i da kasashe lasisin buga ingantaccen kwafin Al-Kur'anin da kwamatin ya tantance. Duk da cewa asalin haddar Al-Kur'anin ana dogara ne da lakantawa mai koyo da fatar baki, sai dai Sheikh Imad Muhsin ya ce shi ma rubutun na Al-Kur'anin na da nasa muhimmancin.
Bayan Al-Kur'anin da ake bugashi a takarda, kwamatin ya tsara wata manhajar Computer da ke iya gyara Al-Kur'anan da ake anfani da su kafar Internet da manhajojin koyar da haddar Al-Kur'ani mai girma, domin tabbatar da ganin cewa ba a koyar da yara ko masu koyo da Al-Kur'anin da akai kuskure wajen rubuta shi ba.