050209 Sicherheitskonferenz München
February 6, 2009Taron harkokin tsaro na birnin Munich, taro ne da Jamus take matuƙar martabawa idan ana batun manufofin tsaro. Daga ranar 6 zuwa 8 ga wannan wata ƙwararrun masana da kuma 'yan siyasa za su sake taruwa domin tattauna batun harkokin tsaro a duniya. Daga cikinsu akwai shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel da Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy da kuma mataimakin shugaban ƙasar Amirka Joe Biden.
Taron wanda aka fara shi yau juma'a da yamma, wanda kuma Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya buɗe, taro ne da ya saba karɓar baƙuncin manyan mutane, wanda kuma a duk lokacin da aka gudanar da shi, to akwai wani mutum da ake kallo a matsayin jigon taron wanda za a zubawa idanu a ji mai zai ce. To a wannan karo jigon wannan taro na birnin Munich shi ne mataimakin Shugaban ƙasar Amirka Joe Biden. Wanda tuni daraktan taron Wolfgang Ischinger ya fara yabon yunƙurin na Amirka.
“Ya ce Ina mai matuƙar alfahari da yadda gwamnatin Amirka ta ƙuduri aniyar fara nuna tasirinta akan harkokin waje da na tsaron waɗansu ƙasashe dake nesa da Amirka, musamman ma a birnin munich dake nan Jamus. Wannan abin yabawa ne''
Joe Biden dai zai fuskanci jarrabawa guda biyu a wannan tafiya ta farko akan batun harkokin waje da wani babban jami'in gwamnatin Obama ya yi tun farkon kafuwarta. Shin ko zai iya jan hankalin Nahiyar Turai su yarda da manufofin Amirka akan Afganistan, tare gamsar da nahiyar Turan ta yarda ta bunƙasa taimakonta akan wannan ƙasa da ma yankin Gabas ta tsakiya baki ɗaya? Shin ko zai iya samun karsashin yin gamsasshen bayani a gaban gogaggun shugabanni masu ra'ayin bin diddigi da son jin ƙwaƙwaf? To sai dai a zuba ido a gani.
Wani batu kuma da ake sa ran zai ɗauki hankalin taron shi ne batun tattaunawar kai tsaye da ƙasar Iran tsakanin shi Joe Baden ɗin da kuma mahukuntan Iran. Elke Hoff (FDP) masaniya ce akan harkokin tsaron Jamus
“Burin da gwamnatin Obama take da shi na miƙa hannu bi-biyu ga ƙasar Iran domin tattaunawa ta kai tsaye bisa manufa, ita ce kaɗai hanya mafi dacewa domin cimma nasara. Ko da dai babu shakka za mu jira mu gani ko wannan tafarki zai haifar da Ɗa mai idanu. Kuma a gaskiya ma dai tattaunawa da Iran cikin lumana ita ce a'ala, amma ba mummunar mu'amalar da za ta jefa mutane cikin tashin hankali ba''.
Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya buɗe taron ne da batun kiyaye bazuwar makamai, wanda a ciki aka taɓo batun na Iran;
“Ya ce Muna so mu tabbatar da cewa duk wata ƙasa da take da burin bunƙasa harkokin fasaharta, to za ta yi hakan ne a ƙarƙashin kulawar ƙasa da ƙasa, idan zai yiwu ma a ce a komai ya kasance karkashin hukumar nan ta (IAEA). Kuma wannan ƙuduri yana ci-gaba da samun karɓuwa. kuma za mu ci-gaba da angiza shi iya iyawarmu. Kuma tattaunawata ta gaba da zan yi ma, zan yi ta ne da shugaban hukumar ta IAEA El Baradei a ƙarshen mako mai zuwa a Munich''.
Akwai dai batutuwa na harkokin tsaro da dama da za a tattauna a taron na birnin Munich.